Mafi yawan jarumai a masana’antar Kannywood na amfani da kafafen sada zumunta musamman shafukan Facebook, Tik Tok da kuma Instagram inda sukan dora hotuna, bidiyo da sauran tallace tallace da a kan ba su lokaci bayan lokaci.
Ta wannan hanyar masoyansu da dama kan bibiye su a shafukan domin sake kulla dankon soyayya a tsakaninsu, galibi jarumai mata da maza sukan yi amfani da shafukan sada zumunta domin su kara yawan masoyansu ta hanyar kyawawan hotuna da faya fayen bidiyo don duk su burge mabiya da masoyansu.
- Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?
- Fina-finai Masu Dogon Zango Koma Baya Ne Ga Masana’antar Kannywood – Tanimu Akawu
A wannan makon Leadership Hausa ta bibiyi shafukann wadannan sanannun jarumai a masana’antar ta Kannywood domin zakulo maku wadanda suka fi saura yawan mabiya a wannan saha ta sada zumunta musamman Facebook, Tik Tok da Instagram.
(10). Abdullahi Amdaz
Mabiya Miliyan 2
Wannan jarumin ba boyayye bane a masana’antar Kannywood domin kuwa bayan zamansa jarumi ya na kuma taba wakoki,ya yi shura a shekarun 2022 a lokacin ya fito a cikin shirin fim mai dogon zango na Labarina, rawar da ya taka a wannan shiri ya sa ya tara dimbin masoya a ciki da wajen Nijeriya hakan ya janyo mashi mabiya Miliyan 2 a dukkan kafafen sada zumunta da yake amfani dasu.
(9). Dauda Kahutu Rarara
Mabiya Miliyan 2.4
Mawakin siyasa wanda kuma a wani lokaci yake taba wakokin soyayya a cikin fina finai Dauda Kahutu Rarara, ya tara dimbin masoya sakamakon wakokinsa na siyasa da fina finai, da yake ita siyasa mugun wasa ce inji bahaushe zaman Rarara mawakin siyasa ya sa ya tara masoya kuma a lokaci guda makiya amma duk da hakan bai hana ya samu mabiya Miliyan 2,400,000 ba a shafukansa na Tik Tok, Facebook da kuma Instagram ba.
(8). Maryam Booth (Dijangala)
Mabiya Miliyan 2.7
Maryam Booth ko kuma Dijangala kamar yadda wasu suke kiranta ta samu daukaka tun bayan fitowarta a cikin wani shiri mai suna Dijangala tare da jarumi Adam A Zango, tun lokacin tauraruwarta ta ci gaba da haskawa duba da cewa kyakkyawar matashiyar ta na taka rawar gani a duk bangaren da aka saka ta a cikin shirin fim, Dijangala ta samu mabiya Miliyan 2,700,000 a shafukan sada zumunta uku da take amfani dasu.
(7). Nafisa Abdullahi
Mabiya Miliyan 2.8
Nafisa Abdullahi jaruma ce da ta amsa sunanta a masana’antar Kannywood, ta fito a manya manyan fina finai da suka samu daukaka a Duniyar fina finan Hausa, ta haka ne jarumar ta yi suna kuma ta samu dimbin masoya, daga cikin manya manyan fina-finan da jarumar ta fito akwai Marainiya,’Ya Daga Allah, Labarina da sauransu bayan shura a fagen shirye shiryen fim jarumar kuma tayi amfani da wannan dama wajen tara mabiya a shafukan sada zumunta inda ta ke da mabiya fiye da 2,800,000 a shafukanta na Instagram da Tik Tok.
(6). Aisha Humaira
Mabiya Miliyan 4.1
Aisha Humaira ta shahara musamman a manhajar Tik Tok da Instagram inda ta ke dora gajerun bidiyoyi masu kayatar da mabiyanta, Aisha wadda ta ke da kusanci da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a lokuta da dama a kan ganeta ta na dora gajerun bidiyoyin wakokin siyasa musamman wadanda Rarara ya rera da kanshi, a fagen fina finai jarumar ta zama mai daukar nauyin fina finai (furodusa) inda ta shirya fim dinta na farko mai suna A Cikin Biyu jarumar tanada mabiya Miliyan 4,100,000 a shafukanta na Tik Tok da Instagram.
(5). Adam A Zango
Mabiya Miliyan 4.1
Daya daga cikin jarumai maza da suka dade ana damawa dasu a wannan masana’antar ta Kannywood Adam A Zango, jarumi kuma mawaki ya shafe shekaru fiye da 10 ana ganinsa a cikin manyan fina-finai, ba iya waka da fim kawai Adamu ya tsaya ba hakazalika ya na taba harkar kasuwanci a gefe a kafar sada zumunta kuwa Adamu ya tara mabiya da suka haura 4,100,000 a shafukan sa na Tik Tok,Facebook da shafin Instagram.
(4). Naziru Ahmed (Sarkin Waka)
Mabiya Miliyan 4.3
Mawakin sarakuna da wakokin soyayya Naziru M Ahmed wanda ake kira da Sarkin Waka ya yi shura a kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram da Tik Tok, lokuta da dama mawakin ya kan janyo cece kuce a wadansu rubuce rubucensa kokuma abubuwan da yake dorawa a shafukanshi,kwanakin baya mawakin a wata hira da yayi ya kira matasa masu yin harkar mining na kirifto da suna cima zaune wanda ya matukar bata rayuwar da dama daga cikinsu inda suka dinga kiranye akan mahukuntan Facebook su rufe shafin sarkin wakar, hakan bai hana shi tara mabiya 4,300,000Â a dukkan shafukansa uku ba.
(3)Â Â Rahama Sadau
Mabiya Miliyan 4.9
Rahama Sadau ba sabon suna bane a kunnuwan masu sha’awar kallon fina finai hakazalika ba sabuwar fuska ba ce ga masu sha’awar kallon fina finan Hausa da ma na kudancin Nijeriya,Sadau ta zama kallabi a tsakanin rawuna tun lokacin da ta fara wannan harka ta shirin fim,ba a arewacin Nijeriya kadai ba har da kudancin kasar da ma kasashen waje duka sun san wacece Sadau,da haka ne ta yi amfani da damarta ta hanyar samar wa kanta mabiya Miliyan 4,900,000 a shafukan Facebook, Tik Tok da Instagram.
(2). Hadiza Gabon
Mabiya Miliyan 5.8
Shahararriyar jaruma a masana’antar Kannywood Hadizatu Aliyu kokuma Hadiza Gabon kamar yadda akafi saninta,ta na daya daga cikin manya manyan jarumai da suka ribaci daukakar da Allah ya basu ta hanyar samar wa kansu dimbin masoya a ciki da wajen Nijeriya,Gabon wadda ta shafe shekaru 10 ana damawa da ita a wannan masana’antar ta tara dimbin mabiya a shafukan sada zumunta musamman shafukan Facebook, Tik Tok da Instagram har ta zamo ta daya ga yawan mabiya a shafukan sada zumunta a cikin mata a masana’antar Kannywood ta biyu kuma ga baki daya inda ta ke da mabiya 5,800,000.
(1). Ali Nuhu
Mabiya Miliyan 7.8
Ba abin mamaki bane Sarki Ali Nuhu ya kasance wanda yafi yawan mabiya a shafukan sada zumunta a cikin jaruman masana’antar ta Kannywood,shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya Ali Nuhu Muhammad ya dade ya na jan ragamar wannan masana’antar ta fannin daukaka da sanayya a tsakanin tsararrakinsa jarumai,Sarki kamar yadda ake mashi lakabi ya kasance mutum na farko a duk masana’antar Kannywood da yake da yawan mabiya inda yake da yawan mabiya 7,800,000 a dukkan shafukanshi na sada zumunta da suka hada da Facebook, Tik Tok da Instagram.