A yayin da kalubale daban-daban na yau da kullum ke barazana ga al’ummomi a fadin duniya, yana da mahimmanci a sani cewa, babu wata kasa daya tilo da za ta iya maganin wannan barazanar. Kungiyoyin ‘yan ta’adda na tada zaune tsaye a wasu sassan duniya, wanda ke tilasta wa al’umma yin hijra zuwa wasu kasashe, sannan akwai mummunan sauyin yanayi kamar ambaliyar ruwa, fari, gobara, matsanancin zafi da sauransu wanda ba su bambance kimar kasa, mai Arziki ce ko akasin haka.
Duba da haka, akwai bukatar hadin kai a tsakanin kasashe baki daya ba tare da nuna wariya ba don tunkarar irin wannan barazana.
- Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
- Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)
Kasar Sin ta kasance a ko da yaushe a gaba wajen kira ga takwarorinta na duniya wajen tunkarar kalubalen duniya don ganin an hada kai an magance matsalolin da ke barazana ga ci gaban dan Adam da ma duniya baki daya.
A taron kungiyar kasashen G20 karo na 19 wanda ba a jima da kammalawa ba a Rio de Janeiro, babban birnin Kasar Brazil, shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya yi kira da babbar murya a kan yadda kasashe za su hada kai wajen tabbatar da adalci a duniya.
Kamar yadda ya fada a jawabinsa a zaman taron da aka yi, Shugaba Xi ya ce bai kamata kasashe masu ci gaban tattalin arziki su bar son ci gaban kasashen nasu ya toshe musu tunaninsu ba, domin ya dace a kalli duniya a matsayin al’umma daya mai makoma daya.
Tabbas abin da shugaban ya haska wa mahalarta taron yana bukatar aiwatarwa cikin hanzari, domin babu yadda za a samu kwanciyar hankali da wadata yayin da mai arziki ke kara kudancewa, talaka kuma ke kara talaucewa, ya kamata kasashe masu samun tattalin arziki su rike hannun kasashe masu tasowa don ganin an gudu tare an tsira tare.
A kullum yana daga burin kasar Sin a tabbatar da adalci a duniya, ta fuskar kasuwanci da cinikayya mai ‘yanci domin ta haka ne za a iya karfafa kasashe masu tasowa don su ma su shigo a dama da su a fagen ci gaban zamani.
Kiran da Shugaba Xi ya yi a wurin taron, ba na fatar baki ba ne kawai. Daya daga cikin shaidar hakan shi ne, a kwanan baya an ruwaito ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar ta bakin darakta janar mai kula da kawance tsakanin Sin da Nijeriya, Mista Joseph Tegbe, yana cewa, “A cikin shekarun da suka gabata, mun ga gagarumin ci gaba a fannoni kamar kayayyakin more rayuwa, kasuwanci, makamashi, lafiya da ilimi. Dangantakarmu ba ta tsaya kan ci gaban tattalin arziki kadai ba, har ma da samar da damammaki da za su amfani kasashen biyu da kuma jama’arsu.” Har ila yau, shugaba Xi Jinping ya zayyano matakai guda takwas da kasarsa za ta dauka domin ci gaban duniya a cikin jawabin nasa, ciki har da inganta hadin gwiwar Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, aiwatar da tsare-tsaren ci gaban duniya, tallafa wa bunkasa Afirka, ba da taimako ga hadin gwiwar kasashen duniya a kan rage fatara da samar da wadatar abinci da sauransu.
Tun daga taron koli na G20 da ya gabata a Hangzhou a shekarar 2016, kasar Sin ta sanya ci gaba a matsayin ginshikin habaka manufofin tattalin arziki na G20 a karon farko, kuma taron kolin ya rungumi shirin aiwatar da shirin G20 kan ajandar dorewar ci gaba a shekarar 2030 da shirin G20 kan tallafa wa masana’antu a Afirka da kasashe masu raunin tattalin arziki. Taron Rio na bana ya mayar da hankali kan gina duniya mai adalci wadda za ta dore.
Nasarar da aka samu a taron na kulla kawancen yaki da yunwa da fatara a duniya ya nuna an fara daukar darasi daga kiraye-kirayen da kasar Sin ke yi a duniya da kuma yadda take tafiyar da harkokinta na cikin gida. Kasar Sin ta yi nasarar kawar da matsanancin talauci a tsakani daruruwan miliyoyin al’ummarta.
Hikimar da Shugaba Xi ya yi amfani da ita wajen yi wa mahalarta taron allura a kan daidaita tsarin tafiyar da duniya ta ishi kowa ya yi wa kansa hisabi ya dauki hanyar da za ta bulle masa, domin kamar yadda shugaban ya ce, “Tafiya mai nisan mil dubu tana farawa ne da takun farko,” kuma kasar Sin a shirye take ta yi tafiya da kowa domin samar da duniya mai adalci don cin moriyar juna.”
Kuma yana da kyau a lura da cewa, babu wata kasa da za ta iya tabbatar da tsaronta ta hanyar rikita zaman lafiyar wata kasa, mutuntawa tare da ganin kimar kowacce al’ada ke tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomi kamar yadda Shugaba Xi ya sha nanatawa a galibin kiraye-kirayensa na tabbatar da wanzuwar adalci a doron kasa.