Arewacin Nijeriya, musamman arewa maso yamma na fama da matsanancin kalubalen tsaro na garkuwa da mutane da kashe-kashe sakamakon barnar ‘yan bindiga ko kuma ‘yan fashin daji kamar yadda wasu ke kiran su a yanzu.
Matsalar ‘yan fashin daji dai ta fara kunno kai gadan-gadan ce a shekarar 2011, biyo bayan rikice-rikicen manoma da makiyaya da aka fara samu a arewa maso yammacin Nijeriya. ‘Yan fashin daji a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina sun zama babban barazana ga zaman lafiya a ‘yan shekarun baya. Sun addabi kauyuka da daman gaske.
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
- Asibitin Gombe Ya Haramtawa Ma’aikata Yin Kiripto Lokacin Aiki
Zuwa yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da kokarinsu na kawo karshen masu garkuwa da mutane a arewa. Lamarin da ake samun nasarori duk da cewa a wasu lokutan su ma sojoji na rasa rayukansu a kokarinsu na dakile ‘yan ta’addan.
Jiragen yakin sojojin kasar sun kaddamar da hare-hare daban-daban kan maboyar ‘yan bindigan kuma an samu nasarorin sosai.
A watan Mayu, ministan tsaro Muhammadu Badaru Abubakar ya ce ta hanyar hadin guiwar aiki tsakanin shugabannin hukumomin tsaro da takwarorinsu an samu nasarar kashe ‘yan fashin daji da ‘yan ta’adda sama da 9,300, yayin da aka cafke wasu 7,000 tun a shekarar da ta gabata.
A baya-bayan nan, rundunar sojin Nigeriya ta kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan fashin daji kuma mai sarrafa makamai Kachalla Halilu Sububu, a cikin samamen da suke kaddamarwa kan ‘yan fashin daji a arewa maso yamma.
Sububu, wani jigo ne a harkokin fashi da makami kuma ya mallaki wani katafaren wurin hakar ma’adinai a Dan-Kamfani da ke karamar hukumar Anka, sannan ya mallaki dubban shanu a dajin Sububu.
Kazalika, wasu ‘yan fashin daji da dama ne sojoji suka ayyana nemansu ruwa a kallo bisa shiga harkokin da suka shafi ta’addanci. Jerin kasurguman ‘yan fashin daji da sojoji suka halaka sun hada da
Halilu Sububu da Buhari Alhaji Halidu wanda aka fi sani da “Buharin Yadi”, gawurtaccen dan ta’adda ne da ya addabi jama’a a Kidandan/Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa, Sabon Birni da Kerawa a karamar hukumar Igabi da wasu sassa da dama da suke iyaka da karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina da kuma wasu sassan Jihar Neja da Zamfara.
Akwai kuma wani shugaban ‘yan garkuwa da mutane da ake kira da Dangote ya bakwancin lahira a wani artabun da suka fafata da sojoji a sansani Kachalla Dankarami da ke kusa da dajin Dumbunrun a tsakanin Batsari da karamar hukumar Jibiya na Jihar Katsina.
Boderi Isyaku, fitaccen shugaban masu sace mutane don neman kudin fansa, wanda ya jagoranci garkuwa da daliban kwalejin neman dazuka su 39. Kuma shi ne ya shirya kai hari a kwalejin horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna a 2021, wanda shi ya bakonci lahira.
Sannan akwai Kachalla Dan Chaki da Dogo Gudali da Dogo Rabe, wanda aka kashe shi ne wani harin da sojojin suka kai a ci gaba da share ‘yan fashin daji da suka addabi al’ummar Zurmi da Birnin Magaji a Jihar Zamfara da kuma yankin Jibiya a Jihar Katsina.
Alhaji Auta da Kachalla Ruga dukkaninsu sun bakwancin lahira tare da wasu mambobin tawagar a lokacin da aka yi ram da su a dajin Gusami da kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.
Rufai Maikaji, shi kuma kusa ne da ya jagoranci kashe mutane da dama a harkokin garkuwa da mutane. Shi ma ya bakwancin lahira.
Ya’u, an kashe shi a wani kwantan bauna da sojoji suka kai musu a dajin Burra da ke karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi. Shi din shugaban gungun ‘yan fashin daji ne masu dauke da muggan makamai da suka addabi jama’a a Burra da makwabtanta da garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe.
Alhaji Karki, shi ma ya mutu a lokacin da ya yi arangama da sojoji a Jihar Neja. Karki, wanda ya yi tirjiya daga baya sojojin sun sha karfinsa, shi addabi al’umman Neja da ta’addanci kama daga garkuwa da mutane da neman kudin fansa da sauransu.
Shugaban ‘yan fashin daji “Yellow” ya jagoranci masu garkuwa a sansanin daban-daban da suke Zamfara, Kaduna, da Katsina, ya bakwancin lahira bayan da sojojin suka yi luguden wuta a jihohin Katsina da Zamfara.