Wakilai daga jihohin Jigawa da Katsina da suka halaccin taron wayar da kan jama’a na yakar auren jinsi da cibiyar koyar da addinin Musulunci (IIIT) ta shirya a jami’ar Bayero da ke Jihar Kano, sun sha alwashin hada hannu da cibiyar wajen yakar auren jinsi a kasar nan.
Wakilin gwamnatin Jihar Jigawa, Hamisu Yusuf Abubakar, daraktan mai kula da shashin shari’a a ofishin sakataran gwamnatin Jigawa, ya ce a kokarin gwamnatin Jigawa na ingata harkar tarbiyya da bunkasa ilimin addini da na zamani karkashin Gwamnan Malam Umar Namadi Danmodi ba za ta lamunci auren jinsi ba.
- An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla
- Abinda Ya kamata ku Sani Game Da Sabuwar Shugabar Jami’ar Abuja
Ya ce shi ya sa gwamnatin Jigawa za ta hada hannu da cibiyar koyar da addinin Musulinci a kowane fanni na rayuwa wajen dakile lamarin.
Cibiyar IIIT karkashin shugabancin, Dakta Saidu Ahmad Dukawa, ta shirya taron ne domin yakar yada akidar auren jinsi da makiya addini ke bin salo da dabaru wajen yada wannan mummunar akida a tsakanin kasashen duniya, musamam kasashen Musulmai.
Shi ma babban wakilin gwamnatin Jihar Katsina a wajen wannan taron, Baristar Abdurahman ya ce gwamnatin Dakta Diko Ridda, ba ta wasa da harkar tarbiyya da ilimin addini da na zamani, domin haka a shirye take wajen hada hannu da dukkanin masu san inganta ilimi da tarbiya a Katsina.
A nasa jawabin, shugaban cibiyar Dakta Saidu Ahmad Dukawa, ya ce yaki da irin wadanan miyagun akidu na makiya addini Musulunci da daukacin al’ummar duniya aiki ne na kowa da kowa.
An dai gabatar da dogon jawabi ta yadda ake amfani da kafufin sadarwa da litattafai da sauransu wajen yada wannan akida ta auran jinsi wadda ke barazanar kawar da wanzuwar Dan’adam a doran kasa, wacce ita ce akida mafi muni da ke tunkarar duniya kamar yadda Farfesa Salisu Shehu, ya bayana a cikin kasidar da ya gabatar a taron.