ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Suka Fi Jan Hankali A Taron Koli Na Tsaro A Katsina

by El-Zaharadeen Umar
2 years ago
Katsina

Taron tsaro da zaman lafiya da gwamnonin arewa maso yamma da hukumar UNDP suka shirya a Katsina ya bar wasu tambayoyi a bakin jama’a da dama.

Shin ko wannan zai sha bambam da irin wanda aka saba yi a baya, ko kuwa dai shi taron shan shayi ne irin wanda jama’a ke kallo ana bata dukiyar al’umma ba tare da ganin sakamako ba.

  • An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla
  • Ƴansanda Sun Kama Matar Da Ta Sheƙe Mijinta Har Lahira A Yobe

Taron dai kamar yadda aka bayyana cewa babbar manufarsa shi ne lalubo hanyar warware matsalolin tsaro da ya addabi yankin arewa maso yamma.

ADVERTISEMENT

Tunda farko hukumar UNDP da gwamnonin arewa maso yamma suka dauka nauyin shirya taron domin tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki a kan sha’anin tsaro domin samun mafita baki daya.

Yana da kyau mu gane cewa an sha yin irin wannan taro da niyyar kawo karshen ‘yan bindiga da suka kassara yankin arewa ta fuskanci noma da tattalin arziki da kuma ilimi.

LABARAI MASU NASABA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

A wannan taron akwai sabbin abubuwan da suka bayyana a wajen taron wanda ake ganin kila a samu canji daga abinda ake tsammani da suka fara a baya, ma’ana dai ba taron shan shayi ba ne.

Salon da wannan taro ya zo da shi ya nuna cewa akwai wasu sabbin abubuwa da ba a saba gani ba akan matsalar tsaro.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu wanda shi ne baban bako a wajen taron ya bayyana cewa za su canza salon yadda ake yaki da ‘yan bindiga, inda ya kara da cewa za su yi amfani da karfin soja da kuma tattaunawa ta diplomasiya.

Bola Ahmad Tunibu wanda mataimakinsa Kashim Shattima ya wakilta ya ce gwamnati ba za ta taba barci da idanu biyu ba, har sai ta ga harkar tsaro ta inganta a Nijeriya musamman yankin arewa.

Shin da gaske gwamnatin tarayya ke yi a kan wannan batu, lokaci ne alkali tunda an dade ana ruwa kasa tana shanyewa, batun kyautatawa jami’an tsaro da samar kayan aiki na zamani da biya masu duk bukatu na su ne kadai hanya da zata taimaka wajen rage wannan matsala

Haka suna wasu gwamnoni da suka hau kujerar naki a kan batun yin sulhu da ‘yan bindiga sai gashi suna maganganu masu cin karo na juna.

Kazalika masana na kallon wannan taro bai amsa sunansa ba, na taron zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso yamma musamman kalaman Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda da ya ce ba wanda zai gaya maka matsalar ka fiye da wanda abin ya shafa.

Hakika wannan magana haka take, kuma masana da sauran al’umma sun sa ido su ga idan haka za ta fara a wajen wannan taron, kowa ya yi tunanin cewa za a ga wadanda wannan bala’i ya shafa sun zo gaban masana sun bayyana irin yadda wannan al’amari ya shafe su.

Ko shakka babu, akasin haka aka gani a wannan taron, saboda haka ne gwamnan ya ce suna kokarin gano musabsbin wannan matsala ta tsaro tare da tabbatar da an samu mafita a karshen taron.

Malam Dikko Umar Radda ya ce sun fara gano musabbabin wannan matsala wanda baban abin shi ne talauci da rashin ilimi wanda ya ce dole su hada hannu wajen ganin an magance shi baki daya.

Ya kuma yi amfani da kalma amfani da karfin soja da diplomasiya wanda ake ganin ko ya fara saukuwa daga kujerar naki da ya hau ta cewa ba zai yi sulhu da dan ta’adda ba?

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa yana da tsoron cewa kar fa wannan taro ya kasance irin wanda aka saba yi a baya wato taron shan shayi, ya ce yana kyau mahukunta su tabbatar da cewa daukar mataki shi ne gaba da dogon turanci ba.

Ya kara da idan ba a yi hankali ba, wankin hula yana Iya hukumomi tsaro dare saboda baban aikin da ke gaban su na samar da zaman lafiya a yankin arewa maso yamma da kasa baki daya.

Alfarma Sarkin Musulmi yana magana ne a matsayin wanda ya san sha’anin tsaro kasancewarsa tsohon sojan Nijeriya wanda ya san tsaro da kuma samar da tsaro.

Shi ma a nasa jawabin Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ce akwai bukatar ayi amfani da hanya irin daya wajen maganin wannan matsala domin farfado da wannan yanki da zama koma baya.

Ya kara da cewa gwamnatin sa ta zo da matakai daban-daban da take amfani da su wajen tunkarar matsalar a jihar Zamfara, ya ce irin ta ce ya kamata sauran gwamnonin arewa maso yamma su dauka ayi abu iri daya.

A cewar gwaman Dauda Lawal ya samar da tsarin koyar da sana’o’i ga matasa domin rage zaman kashe wando tare da samar da rundunar tsaro da kuma farfado da harkar Noma da sauran abubuwa.

Wani Abu da ya dauki hankali al’umma a wajen wannan taro shi ne, yadda wasu gwamnoni suka kaurace wa taron amma sun turo wakillai maimakon zuwa da kansu a tattauna da su a yanke hukunci da daukar mataki a gaban su.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ne da na jihar Jigawa Malam Umar Namadi ne kadai gwamnonin da suka halarci taron, amma saura irin su Sakkwato da Kebbi da Kaduna da Kano sun turo wakillai ne kawai.

Rashin zuwan nasu, ya dora alamar cewa ko dai ba su dauki taron da mahimmancin da ake tunani ba, ko ma dai mene ne an yi taron an gama kowa ya kama gaban sa.

Masana da suka halarci wannan taro suna masu hasashen cewa idan har ba a ga wani canji a harkokin tsaron arewa maso yamma ba, to babu shakka wannan taron ba shi da banbanci da saura.

Kazalika sun koka kwarai da gaske da suka ce ya kamata ace wadanda wannan matsala ta shafa sun bayyana a gaban masana da masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro da hukumar UNDP domin a ji irin matsalolin da suke cikin maimakon a tara jama’a ana t zabga turanci.

Wannan tasa aka fara tunanin a karshen taron da suka ce za su da abubuwa guda da suke alaka ta kusa da matsalar ‘yan bindiga domin dora abin a kan faifai kowa ya gani

Daga cikin abubuwan da suka suna sa ran za su fitar a karshen wannan taro shi ne; kara fadada bincike akan musabsbin wannan matsala, fitar da hanyar da za a taimakawa wadanda wannan bala’i ya shafa, sannan za a tabbatar da hadin kan jami’an tsaro da kokarin tabbatar da ingancin tsaro da kuma haka kuma taron zai samar da hanyar karfafa saman lafiya da tsaro

A karshen taron an kafa kwamitin mai wakilai daga kowace jiha mutum daya sai wakilan UNDP mutum biyar inda aka ba su sati uku su fito da tsarin da za a aiwatar a kan sha’anin tsaron.

Katsina
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Batun Kammala Aikin Gina Gidaje 250 Na “Renewed Hope” Ya Bar Baya Da Kura A Jihar Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Yusuf Buhari Ya Halarci Zaɓen Fidda Gwani Na Sanatan Shiyyar Daura
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mace Ta Doke Namiji A Zaɓen Fidda Gwani Na Majalisar Tarayya A Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Gayyato Jakadun Kasashen Waje 17 Ya Kara Wa Bukukuwan Sallah Armashi A Katsina

MASU ALAKA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City
Wasanni

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed
Labarai

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Next Post
PDP A Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Sadiq Wali Da Abacha

Jigawa Da Katsina Za Su Hada Hannu Wajen Yakar Akidar Auren Jinsi

LABARAI MASU NASABA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.