Tsohon dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya bayyana kudirinsa na sasanta manyan ‘yan siyasar jihar guda uku wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje da kuma Ibrahim Shekarau.
Zaura ya ce sulhun zai sauya yanayin siyasar Kano daga rigingimun ‘yan adawa zuwa siyasar ci gaba da za ta iya hanzarta ci gaba, kamar yadda ake gani a Legas da sauran jihohin da ke kan gaba.
- Matsalar Wuta Ta Jefa Wasu Sassan Nijeriya Cikin Duhu
- Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara
Da yake jawabi yayin wani shirin siyasa da aka watsa a gidajen rediyon cikin gida, Zaura ya koka da cewa rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan jam’iyyar na kawo cikas ga ci gaban Kano. Ya jaddada cewa dinke barakar da ke tsakaninsu shi ne mabudin bude kofa ga jihar.
“Siyasar adawa a Kano, kamar yadda ake bugawa a halin yanzu, ba ta da amfani. A shirye nake da in yi kokarin sasanta manyan shugabanninmu guda uku da suka hada da Kwankwaso, Ganduje da Shekarau. Kamata ya yi a saka Jihar Kano a gaba maimakon son zuciya. Idan har aka samu hakan, Legas da sauran jihohi za su zuba ido kan Kano domin samun darussa a harkokin siyasar ci gaba,” in ji shi.
Kokarin sulhunta Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, da kuma Kwankwaso, jagorar jam’iyyar NNPP na kasa, ya ci tura a baya saboda dambarwar siyasa. Yunkurin na karshe ya ci tura lokacin da magoya bayan Kwankwaso suka mara wa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello baya domin ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa. A lokacin, Ganduje ya dage cewa shi uba ne ga duk wanda ke son shiga jam’iyyar APC, kalaman da ake ganin ya kawo cikas ga kokarin sulhu.
Ba Zaura kadai ba ne yake kokarin ganin a samu zaman lafiya a tsakanin ‘yan siyasar guda ukun. Sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da suka hada da dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar a zaben 2023, Murtala Sule Garo da kuma fitaccen dan siyasa, Baffa Babba Danagundi, sun yi irin wannan kira.
Kwankwaso, Ganduje, da Shekarau, wadanda dukkansu sun yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan Kano, suna jam’iyyun siyasa daban-daban, kuma sun ci gaba da yin tasiri sosai a matakin kananan hukumomi, jiha, da kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp