Gwamnatin Jihar Filato ta bayyana aniyarta ta gurfanar da duk wanda aka samu da laifin safarar yara a kananan hukumomi 17 na jihar inda take zargin lauyoyi da malaman addini da asibitoci da hannu a safarar yara a jihar.
Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Caroline Panglang Dafur ce ta bayyana hakan a lokacin da take kaddamar da ofishin kungiyar kare hakkin yara na jiha a Jos.
- Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kara Wa Hukumar NEPC Kudaden Aiki
- CBN Zai Ci Tarar Bankuna Naira Miliyan 150 Da Aka Kama Suna Sayar Da Sabbin Takardun Naira
Ta koka da yadda masu fataucin yara ke tafiya cikin hanzari a jihar, inda ta jaddada cewa a baya-bayan nan gwamnati ta gano wasu kararraki da dama.
A cewar kwamishinan, duk da kokarin da gwamnati ke yi na kawar da cin zarafin kananan yara a jihar, wasu marasa kishin kasa ciki har da masu fada a ji na kawo cikas a kokarinsu na shawo kan matsalar, yana mai jaddada cewa ya zama dole a hada karfi da karfe domin kawo karshen matsalar.
Ta ce, “Za mu gurfanar da duk wanda aka samu da laifin safarar yara a kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 17 na jihar. Na yi farin cikin kasancewa cikin wannan muhimmin lokaci. A halin yanzu, muna da mutane sama da 12 da ake tsare da su, kuma ina gayyatar ku da ku ziyarci wurin don shaida kokarin da muke yi. Wannan batu ya shafi ba kawai daidaikun mutane ba ne har ma da cibiyoyi kamar makarantu, asibitoci, har ma da masu aikin doka. Abin takaici, an samu wasu asibitoci da lauyoyi da masu fada a ji da hannu wajen safarar yara, wanda hakan bai dace ba.
“Muna so mu yi gargadi ga dukanmu a nan. Wasu mutane na iya shiga cikin rashin sani a fataucin yara, suna ganin suna taimakon yara. Amma kafin ka sani, za ka iya samun kanka a cikin matsala ta shari’a. Dole ne mu kasance a fadake da kuma sanar da mu. Gwamnati ta kuduri aniyar kawar da duk wani mai hannu a wannan aika-aika, ba tare da la’akari da matsayinsa ko matsayinsa ba. Wannan gwamnati tana daukar yaki da fataucin yara da muhimmanci, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci cikakken nauyin doka.”
Da take jawabi tun da farko, Ko’odinetan CPN ta jihar, Misis Sandra Chikan, ta bayyana cewa akwai yawaitar cin zarafin yara, da sauran munanan dabi’u da ake musu, don haka akwai bukatar hada hannu da gwamnatin jihar domin magance wadannan matsaloli.
Ta ce, “Wannan shi ne lokacin da za mu kara daura damara. Lokaci ya yi da za mu hada kai, dmoni tunkarar matsalolin da suka shafi yaranmu. Ba za mu iya kara samun damar yin aiki a kebe ba Madadin haka, dole ne mu yi aiki a matsayin hadin kai, hadin gwiwa, gamayyar runduna masu azama.
“Abin takaicin da ke gabanmu shi ne yadda a kullum ake safarar yara marasa adadi a Jihar Filato. A wasu kananan hukumomi a jihar, ana zargin wasu yaran da bokaye, ana cin zarafinsu, kuma a lokuta masu tsanani, ana binne su ko a kashe su. Ba za a amince da wadannan ayyukan ba, ”in ji kodinetan jihar.