Mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa a jihar Kogi a yanzu suna cikin fargaba sakamakon ƙaruwar ruwan da kogin Neja da Benuwe suka yi.
Jihar Kogi na ɗaya daga cikin jihohin da aka yi gargaɗin afkuwar ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta bayyana, ta yadda kogin Benuwe da Neja suka haɗe a jihar.
- Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
- Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025
A lokacin da LEADERSHIP ta ziyarci gaɓar kogin Neja a ranar Talata, yawan ruwan ya kai wani matsayi mai ban tsoro, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan mutanen da ke zaune a gaɓar kogin.
Hassan Jibril wanda ke zaune a yankin Pata da ke fama da ambaliyar ruwa a duk shekara, ya ce a yanzu haka suna cikin fargaba, duk da cewa a ko wace shekara sun saba yin gudun hijira tun bayan afkuwar ambaliyar ruwa ta 2012 da ta mamaye wasu al’ummomi a wasu kananan hukumomin jihar.
Ƙananan hukumomin dake cikin fargaba sun haɗa da Kogi, Ajaokuta, Ofu, Ibaji, Adavi, Bassa da Omala.