Sauye-sauyen da aka samu cikin gomman shekaru baya, sun fi sauye-sauyen da aka samu cikin shekaru dubu a jihar Xizang, wannan shi ne kalmomin da ake amfani da su wajen kwatanta nasarorin ci gaban Xizang.
Canjin da Xizang ta samu cikin shekaru 60 da suka gabata ba kawai ya bayyana tarihin ci gaban yankin na Sin ba ne, har ma yana nuna ci gaban wayewar dan adam. A karkashin jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin JKS, jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kafa tsarin gurguzu da mulkin dimokuradiyya dake shafar jama’a, ta aiwaitar da tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, kuma ta gina al’umma mai matsakaiciyar wadata. A karkashin jagorancin JKS, cikin shekaru 60 da suka wuce, jihar Xizang ta sami cikakken ’yancin gudanar da harkokinta da kanta, wanda ya haifar da karfin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. Babban canjin da ya faru a Xizang ya samo asali ne daga dagewa kan kula da “manyan ayyuka hudu”, wato tabbatar da kwanciyar hankali, samar da ci gaba, kare muhalli, da kuma kiyaye iyakoki, wadanda suka kawo amfanin gaske ga jama’a.
- Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan El Classico Na Yau
- ’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m
Daga habaka masana’antu na musamman na yankin tsaunuka, zuwa ci gaban manyan ayyuka kamar aikin samar da wutar lantarki daga bangare na karshe na kogin Yarlung Tsangpo da layin dogo na Sichuan zuwa Xizang, dagewa ga aikin inganta muhalli, har zuwa habaka sabbin birane da kuma samun cikakken ci gaban kauyuka, dukkan wadannan matakai sun kasance taswirar ci gaban jihar Xizang.
A yau, jihar Xizang tare da sauran yankuna na Sin sun shiga sabon tafarki na gina kasa ta zamani ta hanyar gurguzu. Labarin zamanintar da yankin Xizang zai zama wani sabon babi mai armashi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp