Akalla jihohi 10 na Nijeriya sun kara kinkimo bashin cikin gida na naira biliyan 417.7 a shekara zuwa shekara, duk da cewa an sami gagarumin kari a tsarin kudin da aka ware daga asusun gwamnatin tarayya.
Binciken kan rahotannin kowane kwata na ofishin kula da basuka ya fitar kan bashin jihohin ya nuna cewa jihohin sun hada da Ribas, Inugu, Neja, Bauchi, Benuwai, Gombe, Edo, Kwara, Taraba da kuma Nasarawa, wanda basukan suka karu da naira biliyan 884.9 a watanni uku na 2024 zuwa naira tiriliyan 1.3 a watanni ukun 2025.
- Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
- Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta
Wannan yana nuni da karuwar kashi 47.2 cikin 100 daga shekara zuwa shekara, yana haifar da alamun tambayoyi kan harkokin kudade da dorewar bashin a matakin jiha.
Bayanan kuma sun nuna cewa bashin gida na jihohi 10 yana karu kowane kwata, daga naira tiriliyan 1.26 a wata hudun farko na 2024 zuwa naira tiriliyan 1.30 a watanni uku na 2025, karin naira biliyan 42.3, wanda ke wakilta karin kashi 3.4 cikin dari a cikin watanni uku kadan.
Wannan karuwar bashi ta zo ne a lokacin da jihohi suka kara samun kaso mai tsoka daga asusun gwamnatin tarayya, wanda aka kara samun kadaden shiga ta hanyar karuwar farashin mai, riba daga rage darajar naira, da rarar kudade da aka samu daga cire tallafin man fetur.
Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10.
Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira biliyan 82.48 a farkon wata uku na 2024 zuwa naira biliyan 188.42 a farkon wata uku na 2025, wanda ke nuna karuwa na naira biliyan 105.95 ko kashi 128.4 cikin dari.
Jihar Neja ta biyo baya da karuwar naira biliyan 57.68 a kowanne shekara, daga naira biliyan 86.07 zuwa naira biliyan 143.75, wanda shi ne karuwa na kashi 67 cikin 100.
Jihar Taraba ta nunka bashin cikin gida har sau biyu daga naira biliyan 32.64 zuwa naira biliyan 82.93, wanda hakan ke nuni da karuwar naira biliyan 50.29 ko kashi 154.1 cikin dari a kowace shekara.
Jihar Bauchi ta kara bashinta daga naira biliyan 108.39 zuwa naira biliyan 142.40, wanda ya nuna karuwar kashi 31.4 cikin dari a kowanne shekara.
Jihar Benuwai ta samu karin naira biliyan 13.09 a kowanne shekara, daga naira biliyan 116.73 zuwa naira biliyan 129.82, wanda ke nuna karuwar kashi 11.2 cikin dari.
Jihar Gombe ta kara bashinta ya tashi daga naira biliyan 70.81 zuwa naira biliyan 83.66b a kowanne shekara, wanda ya karu da naira biliyan 12.85 ko kashi 18.1 cikin dari.
Jihar Edo, wacce ke da bashi na naira biliyan 72.38 a farkon wata uku na 2024, ya karu zuwa naira biliyan 82.40 a farkon watanni ukun na 2025, karin naira biliyan 10.02 ko kuma kashi 13.8 cikin 100.
Jihar Kwara ta kara bashinta daga naira biliyan 59.07 zuwa naira biliyan 60.10 a kowanne shekara, karuwa ta naira biliyan 1.03 ko kashi 1.7 cikin dari.
Jihar Nasarawa, ta karawa bashita daga naira biliyan 23.76 zuwa naira biliyan 24.73bn a kowanne shekara, wanda ke nuna karin naira miliyan 968 ko kashi 4.1 cikin dari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp