Yayin da tsadar rayuwa ke ci gaba da ta’azzara, samun abin musamman mai gina jiki ya zama mai matukar wahala a gidaje da dama a Nijeriya.
Tsadar kayan abinci, wani muhimmin ma’auni ne da ke nuna alamun tabarbarewar tattalin arziki, wanda mutum yana ji yana gani ba shi da wani zabi na abincin da zai ci wanda zai gina masa jiki.
A matakin kasa, matsakaicin farashin abinci mai gina jiki; wanda zai iya isar mutum daya ya ci ya koshi a kowace rana, ya kai na kimanin Naira 982 a watan Mayun 2024, inda hakan ke nuna karin da aka samu na kashi 4.7 cikin 100 a watan Afrilu; kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana.
sakamakon banbancin yankunan da ake da su, Yankunan Kudu Maso Yamma; su ne suke da mafi tsadar kayan abinci mai gina jina da kudin ya kai kimanin Naira 1,198, wanda mutum daya zai ci a rana guda, inda yankin Arewa Maso Yamma kuma ke da saukin wannan kayan abinci, domin kuwa duk mutum guda zai kashe Naira 787 kacal a rana guda.
- Wadatar Abinci: Mun Zuba Naira Biliyan 309 Cikin Shekara 1 A Fannin Noma – Ministan Gona
- Yunwa Ta Sa Muka Kashe Wani Yaro Don Samun Na Abinci – Samari
Farashin Kayan Abinci A Shiyoyi Da Jihohi
Hukumar NBS ta bayyana cewa, a matakin jiha; Jihohi Ekiti, Legas da kuma Abiya ne suka fi kowa tsadar abinci mai gina jiki, inda duk mutum guda zai batar da Naira 1,330, 1,249 da kuma 1,215 a jihohin.
Bugu da kari, nazarin bayanai a matakin shiyya ya nuna bambance-bambancen da ake da su a yankuna daban-daban na bangaren sayen abinci mai gina jiki. Shiyyar Kudu Maso Yamma, ya nuna mafi girman tsadar abinci da Naira 1,198 a kowace rana, sai kuma shiyyar Kudu Maso Gabas a kan Naira 1,140; shi ma a kowace rana, inda aka samu akasin haka a shiyyar Arewa Maso Yamma, wadda ke da mafi karancin tsadar wannan abinci a kan Naira 787 a kowace rana.
Haka zalika, farashin abinci mai gina jiki; na wakiltar mafi karancin farashin da ake bukata a dukkanin fadin duniya, ta yadda kowa da kowa zai iya wadatuwa da shi ba tare da wani haufi ba.
Domin kuwa hakan, na bayar da haske ne game da arhar abincin da kuma bayar da damar zabin abinci mai gina jiki ga daidaikun mutane.
Hukumar ta NBS ta yi amfani da bayanai a kan farashin kayan abinci da abubuwan da abincin ya kunsa da kuma ingancinsa ta bangaren gina jiki, wanda zai iya yin gogayya da kowanne a wajen kara lafiya.
An yi amfani da ma’aunin Naira wajen gano jihohi 10, wadanda aka fi samun abinci mai arha da kuma gina jiki a cikinsu, kazalika, ma’aunin na bayar da haske a kan yadda gidaje za su iya samun abinci mai tsada, amma kuma mai gina jiki.
10- Kwara
Matsakaicin farashin abincin da mutum guda zai ci a kowace rana- Naira 838
Kamar yadda aka sani ne, Jihar Kwara na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya, wadda ita ce ta goma a wannan jeri; inda mazauna yankin ke ware kimanin Naira 838 a kowace rana, don cin abincin da zai gina musu jiki; wanda hakan yasa ta zama jiha mafi tsadar abinci a wannan nazari da aka gudanar.
9- Jigawa
Matsakaicin farashin abinci na mutum guda a rana guda- Naira 826
Jihar Jigawa ita ce ta tara a wadannan jerin jihohi, inda mazauna jihar ke kashe kimanin Naira 826 a kowace rana; wajen sayen abinci.
8- Kano
Matsaikacin abin da mutum guda ke kashewa wajen sayen abin a kowace rana– Naira 821
Jihar Kano ce ta takwas a wannan jeri, inda mazauna yankin ke batar da Naira 821, wajen sayen abinci mai gina jiki a kowace rana.
7- Kebbi
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 821
Jihar Kebbi it ace ta bakwai a cikin wannan jeri, domin kuwa ta zo daidai da Jihar Kano; wajen kashe kudi a kan sayen abinci mai gina jiki, wato Naira 821 a kowace rana.
6- Kogi
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 812
Jiha ta shida kuma ita ce Jihar Kogi, inda mazauna cikinta ke batar da Naira 812 a kowace rana, wajen sayen abinci mai gina jiki.
5- Neja
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 810
Jihar Neja ita ce ta biyar cikin wannan jeri, inda mazauna jihar ke ware akalla Naira 810; wajen sayen abinci mai gina jiki, a kowace rana ta duniya.
4- Kaduna
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 777
Jihar Kaduna ce ta zo ta hudu a wannan jeri, inda mazauna yankin ke batar da akalla Naira 777 a kowace rana, don samun abinci mai gina jiki ga kowane mutum guda.
3- Zamfara
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 766
Jihar Zamfara ce ta uku a wannan jeri, inda kowane mazaunin wannan jiha ke kashe Naira 766 a kowace rana, don samun damar cin abinci mai gina jiki.
2- Sakkwato
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 758
Mazauna Jihar Sakkwato, na sadaukar da Naira 758 a kowace rana, don samun abincin da za su ci mai gina jiki.
1-Katsina
Matsakaicin abinci na mutum guda a kowace rana– Naira 739
Jihar Katsina ce jiha mafi arhar abinci mai gina jiki a cikin jerin wadannan jihohi da aka zayyano, domin kuwa suna ware akalla Naira 739 a kowace rana w
ajen samun abincin da za su ci ya gina musu jiki.