Rundunar sojojin saman Nijeriya sun gudanar da sintiri ta sama a kan wasu gungun ‘yan bindiga da aka gano a wasu wuraren da ke cikin jihar Kaduna, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama.
A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar, ya bayyana cewa rundunar ta sanar da gwamnatin jihar Kaduna.
Aruwan ya bayyana cewa, yankin Kawara da ke karamar hukumar Igabi, an gudanar an tabbatar da kashe ‘yan bindiga uku, kuma wasu da aka yi garkuwa da su sun kubuta daga yankin gaba daya.
Sanarwar ta kuma ce a karamar hukumar Chikun, an gudanar da aikin sa ido a Faka, Kangon Kadi, Damba, Ungwan Turai, Galbi, Gwagwada da kewaye inda aka ga ‘yan ta’addan da ke da tazarar kilomita 4 daga Arewa maso Yamma da Godani, kuma an kawar da su.
“A Kuduru, an ga inda ’yan ta’addan suke tare da harba rokoki.
“A karamar hukumar Igabi, an gudanar da ayyuka a garuruwan Riyawa, Alhaji Isiaka, Rima, Riyawa, Rumana, Ungwan Liman, Mai Gishiri da kuma yankin filin jirgin sama na Kaduna,” in ji shi.