Rahotanni daga Najeriya na cewa, matafiyan da suka dade suna jure kalubale na cunkoson tituna da tsawon lokaci da suke kwashewa na yin zirga-zirga a birnin Lagos dake Najeriya, suna matukar farin ciki da jin dadi, da ma sauri na layin dogo da kasar Sin ta gina a birnin, wanda ya fara aiki a ranar Litinin din da ta gabata.
Kamfanin gine-ginen na kasar Sin (CCECC) ya fara gudanar da wannan aiki a watan Yulin shekarar 2010, ya kuma kammala shi cikin nasara a watan Disamban shekarar 2022, kashi na farko na layin dogon ya kai tsawon kilomita 13, kuma ya kunshi tashoshi guda biyar. Kuma shi ne layin dogo na farko da ya ratsa Okokomaiko, yanki mai yawan jama’a a yammacin Legas, da Marina.
A jawabinsa yayin kaddamar da aikin a farkon wannan shekara, gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa, sabon layin dogon zai rage lokacin tafiye-tafiye, da inganta rayuwar jama’a, sannan kuma zai sa Lagos ta kasance daya daga cikin manyan birane na zamani masu juriya a nahiyar Afirka.
A nasa jawabin, manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Legas, Abimbola Akinajo, ya bayyana cewa, bisa tsarin jirgin wanda ake sa ran zai rika jigilar fasinjoji dubu 175 a kullum, zai rika zirga-zirga ne sau 12 a kowace rana na tsawon makonni biyu, kuma sannu a hankali za a kara yawan zirga-zirgar jirgin.(Ibrahim)