Hukumar kula da layin jirgin kasa ta Nijeriya (NRC) ta sanar da dawo da zirga-zirgar jirgin fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna bayan dakatarwar da aka yi a ranar Juma’a.
Daraktan ayyuka na hukumar, Mista Niyi Alli, a cikin wata sanarwa, ya ce, jirgin zai fara jigilar ne a ranar 31 ga watan Janairu.
“Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Nijeriya suna farin cikin sanar da dawowa da jigilar fasinjoji na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
“An dakatar da jigilar ne a ranar 27 ga watan Janairu, sabida sauka da jirgin ya yi akan layinsa a tashar Kubwa a wannan ranar.
“Jirgin zai cigaba da jigilar fasinjoji a ranar 31 ga Janairu, jadawalin yau da kullun – KA2 zai tashi daga tashar Rigasa da misalin karfe 07:00 na safe; AK1 zai tashi daga tashar Idu da karfe 10:00 na safe; KA4 zai tashi daga tashar Rigasa da misalin karfe 1:00 na rana; AK3 zai tashi daga tashar Idu da misalin karfe 4:00 na yamma.
“Sai dai a ranar Laraba, KA2 ne kawai zai tashi daga tashar Rigasa da misalin karfe 07:00 na safe, AK 3 zai tashi daga tashar Idu da misalin karfe 4:00 na yamma,” in ji Alli.