A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu jiragen yakin sojoji suka kashe ‘yan bindiga a kauyen Rarah da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.
An shafe shekaru dai ana kai hare-hare a karamar hukumar Rabah dake gabashin Sokoto.
Yankin dai ya yi iyaka da karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara.
A cewar dan majalisar da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Sokoto, Abdullahi Zakari, sojoji sun harba bama-bamai a wurare uku, wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan ‘yan bindigar.
Ya ce ‘yan bindigar na dawowa ne daga munanan ayyukansu a lokacin da aka harba musu bama-baman.