Rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro (JTF) ta cafke wani mai dakon kaya da hannu wajen rarraba miyagun kwayoyi ga ‘yan bindiga da suka addabi karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi.
Wanda ake zargin mai suna Femi Owoloja, dan asalin Ejiba, an kama shi ne da misalin karfe 7:30 na dare a ranar Asabar a Odo-Eri, daura da hanyar Saminaka, yayin wani sintiri na yau da kullum da JTF ke yi.
- Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya
- Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu
Jami’an tsaron, sun cafke Owoloja ne a yayin da yake safarar haramtattun kwayoyin ga ‘yan bindigar.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin wanda aka ce shi ne Shugaban kungiyar ‘yan acaɓa reshen Ejiba, ya amsa cewa, ya siyo ƙwayoyin ne a wani shagon sayar da magunguna da ke Egbe domin kai wa abokan hulɗar sa da ke cikin dajin.
Babban sakataren yaɗa labarai na shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Adeyemi Babarinde Sunday, ya ce an kuma samu wanda ake zargin da kuɗi har ₦600,000, wanda ake zargin kudaden hada-hadar ta’addanci ne.