Kasashen Mali, Burkina Faso, da Guinea, da ke yammacin Afirka, sun goyi bayan juyin mulki a Nijar, lamarin da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.
Juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso da Mali a baya-bayan nan dai ya samo asali ne sakamakon takaicin yadda hukumomi suka gaza shawo kan ‘yan ta’adda masu ikirarin kishin addinin Musulunci da ke addabar yankin wanda ya hada da kasar Nijar.
Bayan da aka shafe kusan sa’o’i 48 ba a san halin da ake ciki ba a Niamey, babban birnin Nijar, Abdourahamane Tiani, wani janar kuma tsohon maigadin fadar shugaban kasa, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa.
A wani zama na musamman da kungiyar ECOWAS ta gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, karkashin jagorancin shugabanta Bola Tinubu a Abuja, an cimma matsayar sanyawa Nijar takunkumi da dama kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
ECOWAS ta kuma ba da wa’adin mako guda ga sojojin da suka yi juyin mulkin da su mika mulki ga zababbiyar gwamnatin Bazoum.
Ya zuwa yanzu, sojojin sun yi watsi da kiraye-kiraye da dama daga wasu kasashe da kungiyoyin duniya na maido da Bazoum matsayin shugaban kasar.
Kasashe irinsu Amurka da Jamus da kungiyoyi irin su Tarayyar Turai sun dakatar da tallafin kudi da suke baiwa Nijar sabida Allah wadai da juyin mulkin.
Wani bangare na kudurin ECOWAS a ranar Lahadin da ta gabata, shi ne na yin amfani da dukkan matakan da suka dace wajen maido da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar, ciki har da yin amfani da karfin soji idan ba a biya mata bukatunta nan da mako guda ba.
A cikin wata sanarwar hadin guiwa da kasashen Mali, Burkina suka fitar a ranar Litinin, sun gargadi ECOWAS game da duk wani matakin da zai kawo cikas ga zaman lafiyar yankin.
Kasashen sun yi gargadi cewa, amfani da karfin soji a kan Nijar zai tilasta musu su ma su dauki matakan kare kai domin tallafa wa dakarun Nijar da kuma al’ummar Nijar.