Jam’iyyar NNPP ta yi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da ya mutunta girmansa da shekarunsa, ya marawa takwaransa baya dan takarar Jam’iyyar NNPP Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
NNPP ta kuma ce babu wata tattaunawa da ta ke yi da Atiku kan yiwuwar hadewar jam’iyyun na PDP da NNPP a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Haka kuma, ita ma jam’iyyar Labour (LP) ta ce ba ta cikin wata tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar kan yiwuwar hadewa wuri daya.
Da yake magana a wani taron manema labarai a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, shugaban NNPP na kasa, Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar sun damu da furucin da Atiku ya yi kan yiwuwar hadewar jam’iyyun, yana mai jaddada cewa ba su da wata masaniya kan tattaunawar kawance da jam’iyyar PDP.