Iyaye su ne malamai na farko ga yara. A lokacin kuruciyar shugaban kasar Sin Xi Jinping, mahaifiyarsa Qi Xin ta raka shi kantin sai da littattafai, domin sayen littattafai kamar Tarihin Yue Fei, shahararren jarumi a zamanin daular Song ta kudu ta kasar Sin da sauransu, sannan ta fada masa labaran Yue Fei kamar na Bautawa Kasa, da kuma yadda mahaifiyar Yue Fei ta sassaka kalmomi guda hudu masu ma’anar “Bautawa kasa” a bayan jikinsa.
Xi Jinping ya tuna cewa, “Na ce, ‘Idan an sassaka kalmomin, tabbas za a ji zafi sosai!’, mahaifiyata kuma ta ce, ‘Haka ne akwai zafi, amma ya rike su a zuciyarsa.’ Tun daga wancan lokaci har yanzu, kalmomin nan hudu na rike su a zuciyata, kuma sun kasance burin da nake bi a rayuwata.”
- INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta
- Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali
Bayan ya hau kan mukamin shugabanci, Xi Jinping da mahaifiyarsa ba sa iya haduwa akai-akai. Mahaifiyarsa ta kan rubuta masa wasika, inda take gargadinsa cewa ya yi wa kansa kaidi a dukkan fannoni. Ta gaya wa Xi Jinping cewa, “Muddin ka yi aikinka da kyau, wannan shi ne mafi girman biyayya gare ni da mahaifinka.”
Ya girma a cikin kyakkyawar al’adar iyali, kuma ya fito daga jama’a. A ko da yaushe yana ba da mahimmanci ga iyali, da kuma mayar da hankali kan dangantakar iyalai. Ya taba yin nuni da cewa, kyawawan dabi’u na gargajiya na al’ummar Sinawa game da iyali, wani muhimmin karfi ne na ruhaniya da ke tallafawa ci gaban al’ummar kasar Sin daga zuriya zuwa zuriya.
Bisa ga imaninsa na “Kasancewa marar son kai, kuma mai mayar da jama’a a gaba da komai”, yana jagorantar jama’ar kasar Sin sama da biliyan 1.4, wajen samar da wata makoma mafi kyau. (Mai fassaara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp