Zababben gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shawarci bankuna da su daina bai wa gwamnati mai barin gado bashi.
Wannan dai na zuwa ne bayan shawarar da ya bai wa masu gine-gine a filayen gwamnati, makarantu, makabartu da sauransu.
Yusuf ya bayar da wannan shawara kan gine-gine ba bisa ka’ida ba a wurare jama’a.
Sai dai kuma gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ce ya daina zumudi ya bari a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Amma a cikin wata shawara da ya sake bayarwa da ke kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan mai jiran gado, Sanusi Bature Dawakin Tofa, Abba ya jadadda cewar cewa shawarar ta zama dole.
Sanarwar ta ce: “Daga ranar 18 ga watan Maris zuwa 29 ga Mayu, babu wani mai ba da lamuni (na gida ko na waje) da zai amince da bayar da rance ga gwamnatin Jihar Kano ba tare da amincewar gwamnati mai zuwa ba.
“Duk masu ba da rancen kudi ga Gwamnatin Jihar Kano su lura cewa gwamnati mai barin gado na cin bashi ba gaira ba dalili.”
Zababben gwamnan ya zargi Ganduje da ciyo bashi ba gaira ba dalili don darawa gwamnati mai jiran gado wahala.
Ya kara da cewa shawara ya yi ta ne domin amfanin jama’a.