Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce kaddamar da manyan ayyukan raya kasa guda biyu a tarayyar Najeriya, zai bude sabon babi a fannin bunkasa tattalin arzikin kasar, tare da samar da kyakkyawan mafari, na ingiza hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a sabuwar shekarar nan ta 2023.
Mao Ning wadda ta bayyana hakan yau Talata yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce yayin hutun bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta Sin, an yi bikin kaddamar da tashar teku mai zurfi ta Lekki a jihar Lagos dake kudancin Najeriya, da kuma sashe na farko na layin dogo mai aiki da lantarki a jihar ta Lagos, ayyukan da dukkanin su kamfanonin Sin suka gudanar da su cikin nasara.
Da take amsa tambayar da aka yi mata kuwa, game da sauya fasalin bashin da ake bin kasar Zambia kuwa, Mao Ning ta ce har kullum, Sin na dora muhimmanci ga batun bashin da Zambia ta karba, tana kuma aiwatar da matakai mafiya dacewa, na warware batun bashin karkashin “yarjejeniyar bai daya ” ta kasashen kungiyar G20. Kaza lika jami’ar ta jaddada cewa, batun neman ci gaba, shi ne tushen kalubalen bashi a nahiyar Afirka. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)