Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya bayyana irin illar harin da ake kai ofishoshin hukumar gabanin babban zaben 2023.
Yakubu ya yi gargadin cewa jerin hare-haren da ake kai wa cibiyoyin INEC na iya kawo cikas ga zaben 2023 idan ba a yi wani abu a kai ba.
- Za A Yi Jana’izar Tsohon Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Abdullahi Mahdi Da Yammacin Ranar Asabar
- Dansanda Wakilin Nijeriya, Ne Akwai Bukatar Girmama Shi – Osinbajo
Ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake jawabi ga kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken hare-haren da aka kai kan ofisoshi da kayan aikin INEC a Abuja jiya.
Shugaban na INEC ya jaddada cewa, yayin da hukumar ta kuduri aniyar ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zabe, hare-haren da ake ci gaba da kai wa cibiyoyinta na zama babbar barazana.
Yakubu, ya sha alwashin cewa INEC za ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zabukan 2023 duk da hare-haren da aka kai wa cibiyoyinta.
A cewar Yakubu: “Duk da haka, idan irin wadannan hare-hare suka ci gaba da faruwa a irin yadda suke faruwa a halin yanzu, hukumar na iya samun cikas a lokacin zabe.
“Idan har ana maganar dakatar da hare-haren, to za mu iya samun nasara, amma idan aka ci gaba da kai hare-haren, zabe zai yi mana matukar wahala.
“Hare-haren suna da tasiri mai yawa kan shirye-shiryen babban zabe. Na farko, wuraren da aka lalata, musamman ofisoshinmu, za su dauki lokaci kafin a sake gina su.”
Kwanakin baya, ‘yan bindiga sun kai hari ofisoshin INEC a Jihohin Imo, Enugu, Osun, Akwa Ibom, Anambra, Ogun, Legas, Ondo, da Bayelsa.