A jiya Alhamis ne, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Zhang Xiaogang ya bayyana cewa, wasu ‘yan makamai ba za su cike gibin karfin sojin zirin Taiwan ba, kuma tabbas ba za su dakatar da yanayi na tarihi na sake hadewar kasar Sin ba.
Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga tambayar manema labarai kan sabon shirin Amurka na sayar da makamai ga yankin Taiwan na kasar Sin, wanda rahotanni suka ce sun hada da tsarin makami mai linzami da ake harbawa daga doran kasa da na’urar dake gano motsin abubuwa daga nesa wato Radar System.
- Karuwar Tattalin Arzikin Sin Ita Ce Damar Raya Ciniki A Afirka
- Matsalar Almajirai Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta Kalubale Ga Shugabannin Arewa – Sultan
Zhang ya ce, sayar da makaman da Amurka ke yi wa Taiwan ya sabawa manufar kasancewar Sin daya tak, da sanarwoyin hadin gwiwa uku na Sin da Amurka, da dora ‘yan aware na yankin Taiwan bisa mummunar turba.
Kakakin ya kara da cewa, “Amurka ta yi watsi da alkawarin da ta dauka, kuma ta dage wajen ba wa Taiwan makamai, da karfafa gwiwar ‘yan awaren masu neman ‘yancin kan Taiwan, da kuma tunzura Taiwan zuwa ga fadawa cikin rikicin soja,”
Kakakin ya kara nanata cewa, sojojin kasar Sin za su inganta shirye-shiryensu na yaki, da kara karfin fada da cin nasara gaba daya, da kuma kiyaye ‘yancin kan kasa da mutuncin yankunanta. (Yahaya)