An gudanar da taron manema labaru na taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) ta 14, a yau Litinin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, inda kakakin taron Mista Lou Qinjian, ya amsa wasu tambayoyin da manema labaru na kasar Sin da na kasashen waje suka yi masa.
Dangane da batun yankin teku dake kudancin kasar Sin, Mista Lou ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin kare ikonta na mallakar yankunan kasa, da ma yankin tekun ta. A sa’i daya kuma, kasar na son tattaunawa tare da wasu kasashe, don daidaita wasu batutuwan da suka shafe su, don neman tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar bisa hadin gwiwa.
- An Bude Taron Shekara-shekara Na Majalisar Bada Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin
- Shugaban Kasar Saliyo Na Fatan Hadin Gwiwar Aikin Gona Da Lardin Hubei Na Kasar SinÂ
Sa’an nan, game da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, jami’in na kasar Sin ya ce, ana fatan ganin kyautatuwar hulda. Ya ce, tun lokacin baya har zuwa yanzu, ra’ayin kasar Sin shi ne a tsaya kan ka’idoji 3 da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, wato girmama juna, da zama tare cikin lumana, da hadin gwiwa da zummar amfanar juna, ta yadda za a iya tabbatar da ingantuwar hulda mai dorewa a tsakanin kasashen Sin da Amurka. Kasar Sin ta fadi haka, sa’an nan ta aikata abun da ta fada, sai dai tana fatan ganin kasar Amurka ta cika alkawarin da ta yi, da aiwatar da matsaya daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, yayin ganawarsu a birnin San Francisco na kasar Amurka a watan Nuwamban bara, in ji jami’in.
Ban da haka, a game da babban zaben kasar Amurka, Lou ya ce harka ce ta cikin gidan kasar Amurka, saboda haka kasar Sin ba ta da wani ra’ayi a kai. Duk wani mutum da ya ci zaben, kasar Sin na fatan ganin kasar Amurka za ta yi kokari tare da ita, don kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani yanayi mai inganci, da dorewa, ba tare da tangal-tangal ba, a cewar jami’in na kasar Sin. (Bello Wang)