Cikin rubutun da ya gabata, akwai inda aka dan bincina cewa, duba da irin manufofi hada da sauran nauyaye-nauyayen dake jibge bisa wuyayen kungiyar kwadago, NLC, ba abin mamaki ne ba a gan ta dutse a hannun riga tsakaninta da wata gwamnati a Nijeriya, sawa’un, gwamnatin Soja ce koko ta Farar Hula ce!
Daga cikin manufofin dake rubuce cikin kundin tafikad da wannan kungiya ta ma’aikata sun hadar da;
- Yadda Amurka Ke Kwaton Albarkatun Kasa Da Kasa Da Sunan Yaki Da Ta’addanci
- Bauchi Ta Kori CSA Ibrahim Daga Aikin Gwamnati Kan Badakalarr Kudin Fansho
(i) Habaka tare da bunkasa tattalin arzikin ma’aikata da ‘yan fansho a Nijeriya. Haka da kare ‘yanci na siyasa da na zamantakewar ma’aikata da ‘yan fansho a Nijeriya.
(ii) Ci gaba da inganta rayuwar ma’aikaci da bunkasa hanyoyin kara samun kudin shiga ga ma’aikacin, tare da samun sauran ababen more rayuwa a wajen aikin nasa.
(iii) Inganta, tare da samar da yanayin da zai dorar da samun hadin-kai a tsakanin kungiyoyin ‘yan kasuwa a Kasa. Sannan, sai samar da yanayin da zai dorar da dunkulewar kungiyar ma’aikata a Kasa, ba tare nuna wata wariya ta siyasa, ko al’ada, ko asali, ko wani banbancin jinsi a tsakanin ma’aikatan ba.
(ib) Yin aiki don Inganta ci gaban masana’antu da arziki a Kasa. Su kuma tabbatar da kare salwantar aiyukan yi ga ma’aikata, samun cikakken aiki tare da samun mutuntawa ga ma’aikaci a wurin aiki.
Duba da irin wadancan manufofi da kuma nauyin da ke kan waccan hamshakiyar kungiya ta kwadago da aka zaiyana su a sama, shi ne wasu masharhanta ke bijirar da wasu tuhumce-tuhuhumce ko a ce wasu ayoyin tambaya ga kungiyar ta NLC kamar haka;
1- Ko mai kungiyar ta kwadago za ta ce game da ma’aikatan firamare dubu ashirin (20,000) da gwamna El-Rufa’i ya kora daga bakin aiki?. Ko da yake, bayan korar ma’aikatan, kungiyar NLC ta Kasa, da kuma reshenta na jihar ta Kaduna, sun yi wani hargagin daukar mataki game da korar wannan mamakon adadi na wadanda aka raba su da wuraren cin-abincin nasu, to amma a karshen lamari, sai batun ya koma da tamkar malam ya ci shirwa!
Bayan waccan hayagaga da kungiyar NLC ta yi saboda korar wancan tarago na ma’aikata a Kaduna, hauka farin girki, sai El-Rufa’in ya kara jinko wasu dubban ma’aikata a dai jihar ta Kaduna, tare da kara tisa keyarsu zuwa gidajensu, ma’ana, ya kara sallamarsu daga aiki. Da wadancan ma’aikata dubu 20 na farko da Malam Nasirun ya kora, da kuma dubban rukuni na biyu da ya sake yin awon gaba da su, shin, mai kungiyar ta Kwadago ta yi a kai? Ko mai karatu bai nazarci wajibcin kungiyar ta yi wani abu ba, duba da wadancan kunshin manufofin kungiyar da aka gabatar a sama?.
2- Wace fafutuka ce kungiyar kwadagon ta yi, sa’adda malaman jami’a ke amsar hisabinsu da hannun hagu daga tsohuwar gwamnatin tsohon shugaba Buhari, lokacin da suke tsaka da yajin aikin Watanni takwas (8) a Kasa? Rashin yin babban kumaji da ya kamata NLC ta yi lokacin yajin aikin, sai kuma ba ta yi ba, yanzu a jami’o’in, wa ke karbar hisabi da hannun hagun?. Amsa, ‘ya’yan talakawa mana!
Wadancan dubban ma’aikata da El-Rufa’in ya kora, ‘ya’yan wane ne? Amsa, ‘ya’yan talakawa ne mana! Ko akwai ‘ya’yan tsohon gwamna Sen. Makarfi ciki? Ko akwai ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban Kasa, Namadi Sambo ciki? Amsa, duka babu. Ko akwai ‘ya’yan Dino Milaye ko ‘ya’yan Orubebe cikinsu? A’a babu! To amma kuma yanzu, ai ‘ya’yan talakawan ne ke nuna damuwar wai sanatoci sun ki su tantance El-Rufa’in cikin jerin wadanda za a bai wa mukamin minista.
3- Manazartan sun kara kutsawa cikin bayani kamar haka, har kawo wannan lokaci da muke ciki, jihohi 16 cikin wannan Kasa sun ki dabbaka sabon tsarin mafi karancin albashi na dubu 30. Cikinsu akwai jihohin Enugu, Gombe, Imo, Kogi, Kwara da Nassarawa. Sannan kuma, ma’aikatan jihohi irinsu Ogun, Oyo, Plateau, Ribers, Taraba, Kano (kafin gwamnatin NNPP) da Zamfara, na fuskantar matsalar zaftare musu kudadensu na albashi ne a duk wata.
A wasu jihohi irin su Benue da Ekiti da Cross Riber, dubban ma’aikata ne jibge an ki a yi musu karin matsayi na daga likkafar aiki, daga wannan mataki zuwa wancan. Tsakanin wadancan jihohi da aka ki gabatar musu da sabon tsarin albashi, da kuma wadanda gwamnatoci ke musu fince, zuwa wadanda aka ki yi musu karin girma wajen aiki, wace gagarumar rawa ce Kungiyar Kwadagon, NLC ta taka, wajen ganin gyaruwar lamura ko da ha-maza ha-mata?
Ya kamata mai karatu ya rika banbance tsakanin “kumaji” da “haushi”, wanda tarihin Kungiyar ta Kwadago ke cike da, daga lokaci zuwa lokaci. Ashe rashin dabbaka sabon tsarin albashi da wadancan gwamnatocin jihohi 16 suka yi, bai cancanci samun wani katafaren kumaji ba daga Kungiyar ta Kwadago a duk fadin Kasa? Nawa dubu 30 take a wajen ma’aikaci, amma aka haramta masa, duk da katafariyar Kungiyar ma’aikata ta NLC da yake da ita, sai aka wayigari wannan hakki da yake da shi ya tafi a banza a wofi! Don Allah, wajen ma’aikatan wadancan jihohi 16, wane alfanun Kungiyar kwadago za su dorar? Suma jihohin da aka kwashe Shekaru cikinsu har da Kano a nai musu fincen albashi, ko akwai wani cikakken amfanuwa da za su dorar suna yi da Kungiyar ta NLC a jihohinsu?
4- Ashe babu wata rawa ne da Kungiyar Kwadago za ta taka game da batun samun ikon sarrafa kudade da gwamnatocin jihohi suka amshe daga hannun hukumomin kananan hukumomi? Adadin miliyoyin ma’aikatan kananan hukumomi nawa ne ke cutuwa dare da rana sakamakon turmushe kudaden nasu da gwamnoni ke yi?. Wane kumaji ba haushi ba, da aka ji Kungiyar Kwadago ta NLC ke yi, wajen ‘yantar da miliyoyin wadancan ma’aikatan na kananan hukumomi?
Rahotannin masana guda nawa ne da aka kattaba, wadanda ke nuna tasirin rashin mallakar wadancan kudade da kananan hukumomi ke yi, wajen karuwar aiyukan ta’addanci a Nijeriya? Ko kuwa, yunkurin ‘yantar da kudaden kananan hukumomin ba ya daga cikin manufofin kungiyar ta kwadago? Idan kuwa haka ne, ashe alkiyamar ma’aikata a Nijeriya, ta jima da tsayawa tun gabanin wannan lokaci da muke ciki.
5- Daga Shekarar 2015 zuwa lokacin Chief Bola Tinubu, sau nawa ne farashin man fetur ke tashi, kuma wane kumaji ne kungiyar ta NLC ta yi, wajen dakile tashin gwauron zabin karin litar man?
Har tsohon shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kammala wa’adin mulkinsa, farashin litar man fetur a Nijeriya bai kere naira dari (N 100) ba. Amma da hawan Buhari mulki cikin Shekarar 2015 ya kara kudin man zuwa naira dari da arba’in da biyar (N 145) kowace lita. Litar man fetur, a hankali a hankali lokacin tsohon shugaba Buhari, ta wuce naira dari da saba’in, to amma wane irin kumaji ne kungiyar NLC ta yi, na dawo da gwamnatin Buharin bisa sirdi? Koko lokacin Buharin ba a yi mummunan fama da kangin talauci ba a Kasa? Gabanin gwamnatin ta Buhari, wane lokaci ne ma’aikata da waninsu suka shiga cikin yanayi na kangin rayuwa tamkar lokacin, kuma me NLC ta yi, don tsamo da ‘yan’uwanta ma’aikata daga kangin fatarar da suka sami kansu ciki?. Sai aka wayigari kaf lokacin Buhari Shekara 8, ban da haushi, mutum ba shi iya kawo wani kumaji ne daya tak, da za a ce kungiyar NLC ta yi don kawo sawaba ga jama’ar Kasa!
Kira Ga Kungiyar Kwadago, NLC
Babu shakka, duk da irin korafe-korafen da ke fitowa daga bakunan masu sharhin lamuran da ke wakana yau da kullum game da kungiyar ta kwadago, hakan ba zai zama wani dalili na yin tirr da daukacin aiyukan kungiyar ba a Nijeriya. Illa-iyaka, inda kungiyar ta yi daidai, a yaba mata ne, inda kuma ta kauce hanya, sai a ja linzaminta.
Duk da sukurkucewa da za a iya cewa kungiyar ta kwadago ta yi a kan wasu lokuta da suka gabata cikin a wannan Kasa, har yau din nan, babu wata kungiya da a zahirance ke samun sukunin takawa gwamnatoci birkin dole sama da su. Saboda haka, kungiya ce babba, wadda ya dace ta rika dora aiyukanta ne bisa sanannun manufofinta da aka santa da su tun azal. Yin hakan, zai janye zargin da a yanzu ake yi mata, na, birbishin bangarenci da kabilanci tattare da ita.
Kamar yadda ta rika bai wa tsohon shugaba Buhari lokaci gabanin yin wani fito na fito, shi ma shugaba Tinubu na bukatar a ba shi lokaci. Amma hakan, ba yana nufin ja-injar da suke yi da shi yanzu, ta tsagaita ne kwata-kwata ba. Sam, su ci gaba da fafutukar nemawa jama’ar Kasa sawaba ta kowace fuska.
Game da batun janye tallafin man fetur kuwa “fuel subsidy”, yana da kyau ne su kalli batun ta fuskoki mabanbanta. Misali;
(i) Duk cikin manyan ‘yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben Shekarar 2023, wadanda ake tunanin za su kai bantensu, sun yi ikirarin janye wannan tallafi da ake kwarbai a kansa a yau.
(ii) A bi abin sannu sannu, a yi dakon, shin, abubuwan jinkai da gwamnati ta yi alkawarin yi sakamakon janye wancan tallafi, yaya gudanarsu take? A nan, ba a na nufin cewa farashin man fetur ya ci gaba ta hauhawa ba ne, ko yanzu mu na neman sauki ne!
Akwai masu kyautata zato ga sabon shugabancin kungiyar Kwadagon ta Kasa, yana da kyau ne sabon shugabancin ya nuna ya san aikinsa, musamman ta hanyar tsayawa kyam bisa gaskiya tare da kaucewa amsar na-goro, zargin da daman mutane ke yi wa kungiyar, wanda a sakamakonsa ne ma wasu dubban mutane suka dawo daga rakiyar kungiyar tsawon lokaci.
Yana da kyau kungiyar ta rika tafiyar da lamuranta bisa faifai ga jama’ar Kasa, sabgar rufa-rufa ba ta haifar da komai a tsakanin mutane face mugun zargi da kuma kiki-juna.
Cikin dukkan lamura, yana da kyau ne kungiyar ta rika cizawa tare da hurawa. Yanzu haka Duniya na fama da wani irin yanayi ne mawuyaci.
A karshe, a fili ne yake cewa, wani shugabancin na kungiyar ta NLC, ya kan kere wani inganci da jajurcewa. Wani shugabancin, na yin kumaji ne mai ma’ana tare da haife da-mai-ido, yayinda wani shugabancin kungiyar ya shahara ne da gabza haushi marar tasiri kuma abin yi wa tirrr!!!.
Gaba dai, gaba dai Nijeriya! Gaba dai, gaba dai jihar Kano!! Gaba dai, gaba dai kungiyar NLC