Ba wani abu ne ba sabo mutum ya ji mabanbantan ra’ayoyi da al’umar Nijeriya ke da su game da babbar Kungiyar Kwadago ta Kasa, wato NLC. Babu shakka, ra’ayoyin, kan yi hannun riga ne da juna, sakamakon wasu dalilai da ya kamata a nazarce su da idon basira.
Wasu mutane, kan zargi kungiyar ne da raunanan hujjoji, amma dalilan wasu mutanen na sukar kungiyar, sun fi gaban a yi watsi da su cikin kwandon shara. Cikin nazartar wannan dan rubutu, sai Soja ya zamto malamin kansa, ma’ana, sai a ciza ne kuma a hura ido bude!!!.
- Sana’a Komai Kankantarta Ta Fi Maula
- Nijeriya Ta Doke Senegal A Wasan Karshe Na Kwallon Kwando Ta Mata
Samuwar Kungiyar Kwadago (NLC) A Najeriya
Daga dan tarihin da ya zo hannu, an haife wannan kungiya ta kwadago ne cikin Watan Disambar Shekarar 1978, sakamakon maja ko a ce kawance da aka yi tsakaninta da wasu mabanbantan kungiyoyin ‘yan kasuwa da na ma’aikata a Kasar. Tamkar irin yadda aka yi auren siyasar da wasu ke masa kallon auren mutu’a da ya afku a Shekarar 2015 a tsakanin manyan jam’iyyu da kanana a Najeriya, dab da aiwatar da zaben da ya yi silar faduwar gwamnatin PDP, yayinda shugaba Goodluck ya ci damarar yin ta-zarce, daga zangon mulkinsa na daya zuwa na biyu.
Daga cikin kungiyoyin da wannan shahararriyar kungiya ta NLC ta yi wancan kawance da su bayan baiyanarta, sun hadar da kungiyar NTUC (Nigeria Trade Union Congress), LUF (Labour Unity Front), ULC (United Labour Congress, da kuma kungiyar NWC (Nigeria Workers Council). Wadannan kungiyoyi hudu ne mafiya girma a wancan lokacin gabatar da yanayin hadakar, amma, akwai wasu kungiyoyin ma’aikatan masana’antu akalla guda arba’in da biyu (42) da suka aiyana danfaruwarsu da ita kungiyar ta NLC a lokacin kafuwar tata.
Bayan kafuwar kungiyar ta NLC, daga shugabancinta na farko, akwai da yawan mutane da suka fito daga wadancan manyan kungiyoyi hudu da aka lasafta a sama (NTUC, LUF, ULC sannan NWC). Wahab Goodluck ne shugabanta da yai silar samuwarta.
Arangama Tsakanin NLC Da Gwamnatocin Soji
Ga duk mutumin da yai duba na tsanaki ga hakikanin manufofin samar da wannan kungiya ta NLC, la-budda, wajibi ne a rika samun sa-toka-sa-katsi tsakaninta da gwamnatoci musamman irin na Soja. Ba kawai gwamnatocin soja ba, da tafiya ta kara nikatawa kamar yadda za a gabatar nan gaba cikin wannan dan rubutu, an wayigari hatta gwamnatocin farar hula ma ba sa wanyewa lafiya da wannan madigar kungiya ta NLC.
AÂ mabanbantan lokutan gwamnatocin Soji a wannan Kasa, an sha yin kwalli da kai farmaki tare da kame shugabannin wannan kungiya ta NLC, inda za a ga cewa, gwamnatocin, sun fi yin amfani ne da jami’an tsaro na farin kaya (DSS), wajen kai hare haren ga ‘yan kungiyar. Bugu da kari, fakam da yawa, jami’an tsaro kan tarwatsa tarukan ganawa da shugabannin kungiyar ke yi a tsakaninsu. Irin wannan kai sammaci ga’yan kungiyar, ya fi afkuwa ne a lokacin da masu bakin kaki (soja) ke jan ragamar Kasar.
Karkashin mulkin soja a Kasa, ta tabbata cewa, sau biyu ne gwamnatocin soja ke sanya kafa su ce sun ma rushe shugabancin kungiyar ta NLC na kasa kacokan. Ba don komai ba, sai don fito na fito ne da kungiyar ke yi game da wasu manufofin gwamnati da suke fassara su da ba alheri ba ne ba ga al’umar Najeriya, gabanin su fara warware alolarsu da tusa!!!.
Cikin Shekarar 1988 ne gwamnatin Soja karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, aka fara shelanta ruguje shugabancin kungiyar ta NLC. Ba don komai ba, sai don kin goyon bayansu ga wata manufar tattalin arziki da gwamnatin ta samar, wadda aka fi sani da SAP (Structural Adjustment Program). Jin haushin rashin samun goyon bayan NLCn ne ya jaza aiyana soke shugabancinta da gwamnatin IBB ta yi.
Cikin Shekarar 1994 ma, gwamnatin Soja karkashin Janar Sani Abacha, an soke shugabancin kungiyar ta NLC, ba don komai ba, sai don dagewa tare da kumajin kungiyar cewa, lallai ne Kasar ta Nijeriya da ta gaggauta komawa bisa turbar dimukradiyya, sai hakan ya zamto wani babban zunubin da zai wajabta yi wa jagorancin kungiyar rusau. Sannan, wata kitimurmura ta gwamnatocin Soja shi ne, a duk sa’adda suka rushe shugabancin kungiyar na kasa, sai kuma su nadawa kungiyar wani kantoma, don ci gaba da tafiyar da lamuran kungiyar, cikin salon da zai dace da soye-soyen zukatan masu damara, wato Soja.
Cikin Watan Janairun Shekarar 1999, bayan dawowar tsarin mulki irin na dimukradiyya a Kasar ne aka sami sukunin yin wasu gyare-gyare na musamman game da wasu dokoki da suke yin karen-tsaye ga kungiyar ta NLC a lokutan Soja. A wannan lokaci ne aka zabi tsohon gwamna Adams Oshiomhole a matsayin sabon shugaban kungiyar.
Ja-injar NLC Da Gwamnatocin Farar Hula
Tarihin Kungiyar ta NLC bai nuna cewa kawai tsakaninta da gwamnatocin Soja ne ba ta sami rashin fahimtar juna, sam, hatta tsakaninta da masu jagorantar mulkin dimukradiyya a Kasar sun kai ruwa rana! Lokaci ne da Kungiyar ke kan sharafinta da karsashinta, tare da samun kyakkyawar shaida daga akasarin jama’ar Kasa.
A farko farkon Shekarar 2000, an sami wata takaddama tsakanin kungiyar ta NLC da gwamnatin Obasanjo, ba don komai ba, sai don tashin farashin man fetur a Kasar. Wanda hakan ya faru ne sakamakon yunkurin gwamnati na rage adadi mai yawa na tallafi ga man fetur, tare da sallada yin farashin na mai a hannun ‘yan kasuwa’yan jari hujja. Nan take kungiyar ta NLC ta bazama daukar matakan yajin aiki a kai a kai cikin Kasa, a kan hanyarta na tilasa gwamnati yin mi’ara koma baya ga wannan sabuwar manufa tata na rage wani abu daga tallafin na fetur, tare da sallamawa masu manyan masu hada hadar man fetur din a Kasar, jan akalar sanya farashin feturin irin yadda suka so.
Cikin Watan Satumbar Shekarar 2004, kungiyar ta kwadago, ta bai wa gwamnatin Obasanjo wani wa’adin kididdigaggun kwanaki, na, ta canja matsayarta na sanya wani haraji a kan man fetur, ko kuma Kasar ta fuskanci wani gagarumin yajin aiki, duk da cewa wata babbar Kotun taraiya ta fadi cewa, kungiyar ta NLC ba ta da wani hurumi a doka da za ta yi shelar tafiya yajin aiki, kawai don wata manufa da gwamnati ta samar, duk da haka amma, kungiyar NLC, ta shelantawa jama’ar Kasa irin tsare-tsarenta game da tsunduma yajin aikin. A karshe dai jami’an tsaro na farin kaya ne aka yi zargin sun yi ciki da shugaban kungiyar na kasa Oshiomhole, wato sun kame shi.
Sai dai an hakkake cewa, mafi gawurtar zanga-zangar da kungiyar ta yi ita ce ta cikin Watan Janairun Shekarar 2012, a lokacin gwamnatin shugaba Jonathan. Yayinda ya tasamma bin shawarar babban kwamitinsa na tattalin arziki, inda suka hakkake cewa, Kasa na kan tafka asarar biliyoyin nairori game da sha’anin sanya tallafin man feturin. Sannan, aka ga cewa, bayan cire tallafin na mai, farashin litar mai ma zai tashi daga naira sittin da biyar (N 65) zuwa naira dari da arba’in da daya (N 141).
Wancan matsayi da gwamnatin Jonathan ke kokarin dauka, ya jaza kaurewar mummunar zanga-zanga a biranen Lagos da Kano da Fatakwal da sauransu. Wannan irin zanga-zanga da ba a taba gani ba, ta yi silar durkushewar duk wasu sha’anonin tattalin arzikin Kasa. Ala-tilas, sai da shugaba Jonathan ya baiyana yin wurgi da wannan manufa tasa a kafafen yada labarai sannan lamura suka kyautatu, game da wannan zanga-zanga da ake ta faman gabatarwa a cikin sakuna da lungunan Kasar.
Nan da nan mutum ba shi da ikon yankewa wannan kungiya ta NLC hukunci, ba tare da sanin irin nauyayen da ke bisa wuyayenta ba. Bugu da kari, Kungiyar, kan saka jama’ar kasa cikin wasu duffai a wasu lokuta, ta fuskanci kokarin dabbaka hukunci ga wata gwamnati, alhali sun shigar da irin wancan hukunci a mala, sa’adda suka fuskanci wata gwamnatin, alhali nau’in zunubinsu iri guda ne. Yayinda aka fara yin dalla dalla cikin lamuran Kungiyar a nan gaba, akwai yiwuwar mai karatu zai fi fahimtar inda aka sa gaba, ko a ce inda gizo ke sakar!!!.
Mu Hadu A Mako Na Gaba In Shaa Allah