Kungiyar D’Tigress ta Nijeriya ta doke Senegal a wasan karshe na gasar Afrobasket ta mata ta 2023 da aka kammala a kasar Rwanda.
Matan da Rena Wakama ke jagoranta sun lallasa Senegal da ci 84-74 a filin wasa na BK Arena da ke Kigali a kasar Rwanda a ranar Asabar.
- Likitoci Masu Neman Kwarewa Za Su Shiga Zanga-zanga A Nijeriya
- Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 122 A Nijeriya -UNICEF
Nasarar ta sa Nijeriya ta zama kasa ta biyu a Afirka da ta lashe gasar Afrobasket ta mata sau hudu a jere.
Talla