• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kalubalen Da Ke Gaban Real Madrid A Wannan Watan

by Abba Ibrahim Wada
2 years ago
madrid

Bayan da watan Janairu ya kare, Real Madrid za ta buga wasu wasanni masu zafi daga yanzu har zuwa hutun da FIFA kan ware, don fafatawa tsakanin kasa da kasa a cikin watan Maris mai zuwa.

FIFA ta ware wasu lokuta a jadawalin da take tsarawa, don buga ko dai wasannin sada zumunta ko na neman gurbin gasar kofin duniya da sauran su, kuma Real Madrid za ta buga wasa takwas, shida daga ciki a La Liga da kuma a gasar Champions League, fafatawar zagayen ‘yan 16.

  • Real Madrid Ta Dawo Matsayi Na 2 A Laliga Bayan Yin Canjaras Da Vallecano
  • Rashin Cika Alkawari: ASUU Na Gangamin Shiga Wani Sabon Yajin Aiki

Da farko dai Real Madrid za ta karbi bakuncin Girona a Santiago Bernabeu ranar Asabar a gasar La Liga, wasa ne tsakanin Real Madrid, wadda take ta daya a saman teburi da kuma Girona ta biyu.

Kwana uku tsakani, kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta je RB Leipzig, domin wasan farko zagaye na biyu a Champions League, sannan bayan nan Real za ta kara buga wasa a waje a gidan Rayo Ballecano a gasar La Liga mako na 25 ranar Lahadi 18 ga watan Fabrairu.

Daga nan kuma Real Madrid za ta karbi bakuncin Sebilla ranar Lahadi 25 ga watan Fabrairu a Santiago Bernabeu, sannan ta ziyarci Balencia ranar 2 ko 3 ga watan Maris mai zuwa.

LABARAI MASU NASABA

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Daga nan filin Santiago Bernabeu zai karbi bakuncin wasanni masu mahimmaci

ga Real Madrid a shirin da take na taka rawar gani a kakar bana domin za ta fara da karbar bakuncin RB Leipzig a Champions League a wasa na biyu zagaye na biyu ranar Laraba 6 ga watan Maris, karawar da za ta fayyace wacce ta kai kwata fainal a gasar ta zakarun Turai ta bana.

Daga nan Real za ta karbi bakuncin Celta Bigo a wasan mako na 28 a La Liga ranar ko dai 9 ko kuma 10 ga watan Maris, sai wasan karshe da za ta yi daga nan a yi hutu na kalandar FIFA, shi ne wanda za ta ziyarci El Sadar, domin fuskantar Osasuna ranar ko dai 16 ko kuma 17 ga watan Maris.

 

Jerin wasannin da ke gaban Real Madrid:

Real Madrid da Girona, La Liga mako na 24 ranar 10 ga Fabarairu. Leipzig da Real Madrid, Champions League zagayen ‘yan 16 ranar 13 ga Fabarairu.

Rayo da Real Madrid, La Liga mako na 25 ranar 18 ga watan Fabarairu. Real Madrid da Sebilla, La Liga mako na 26 ranar 25 ga Fabarairu. Balencia da Real Madrid, LaLiga mako na 27 ranar 2/3 ga Maris.

Real Madrid da Leipzig, Champions League zagayen ‘yan 16 wasa na biyu ranar 6 ga watan Maris. Real Madrid da Celta, LaLiga mako na 28 ranar 9/10 ga watan Maris.

Osasuna da Real Madrid, LaLiga mako na 29 ranar 16/17 ga watan Maris.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
Wasanni

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya
Wasanni

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko
Wasanni

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
Next Post
AFCON 2023: Kasar Da Ta Lashe Kofi Zata Samu Dala Miliyan 7, Ta Biyu Kuma Dala Miliyan 4

AFCON 2023: Abubuwan Da Suka Faru Gabanin Wasan Karshe

LABARAI MASU NASABA

Matatun mai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.