Alhaji Ibrahim Gusau ya lashe zaben zama sabon shugaban hukumar kwallon kafar ta kasa domin maye gurbin Amanju Pinnick wanda ya kamala wa’adin mulkin sa na shekaru 10 kamar yadda doka ta tsara.
Gusau, wanda dan asalin Jihar Zamfara ne ya do ke Peter sideIdah ne lokacin da aka je zagaye na biyu na kada kuri’u a wajen taron da hukumar ta gudanar a birnin Benin, inda ya samu kuri’u 40 sabanin guda daya tilo da Idahya samu.
- Yadda Ake Tabbatar Da Ci Gaba Mai Inganci A Birnin Shanghai Na Kasar Sin
- Kotun Daukaka Kara Ta Umurci Kungiyar ASUU Da Ta Gaggauta Janye Yajin Aikin Da Take
Bayanai sun ce yan takara irin su Seyi Akinwumi da Shehu Dikko da kuma Abba Yola sun janye daga takarar bayan zagaye na farkona kuri’un da aka kada wanda hakan ne ya ba wa Ibrahim Gusau dammar lashe zaben.
Gusau wanda ya dade yana bada gudumawa wajen jagorancin kungiyoyin kwalllon kafa daban-daban zai fuskanci kalubale sosai wajen dawo da kimar kwallon kafa a Nijeriya, musamman ganin yadda kasar nan ba za ta samud amar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa a kasar Katar ba.
A yanzu dai Alhaji Gusau shi ne zai jagoranci babban kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon kafar kasar nan daga yanzu zuwa shekaru hudu masu zuwa a lokacin da doka ta bayar da dama a sake sabon zabe.
Sai dai sabon shugaban ya samu shugabanci a dai-dai lokacin da kwallon kafar kasar nan take cikin halin rashin tabbas a bangarori da dama wanda hakan ya sa abubuwa da dama suka daina tafiya yadda ya kamata.
Kalubalen da suke gaban Gusau shi ne dawo da Nigeriya babbar kasa a fannin kwallon kafa Dawo da martabar kasar nan a fannin kwallon kafa yana daya daga cikin kalubalen da sabon shugaban zai fuskanta kuma yana bukatar ya gaggauta daukar mataki a kan wannan matsala duba da yadda babbar tawagar kwallon kafa ta kasar ta kasasa mun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a fafata a kasar Qatar.