Kotun daukaka kara ta umarci kungiyar malaman jami’o’i, ASUU da ta gaggauta janye yajin aikin da take gudanarwa.
Sai dai kotun ta amince da bukatar ne bisa sharadin cewa kungiyar ta yi biyayya ga hukuncin da karamar kotun ta yanke sannan kuma ta janye yajin aikin nan take har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.
Kotun ta baiwa ASUU wa’adin kwanaki bakwai da ta shigar da kara biyo bayan bin hukuncin da karamar kotu ta yanke.
Talla