Gwamnatin Jihar Zamfara na ci gaba da tsarin kyautata tsaron cikin gida, ta hangar kafa sabuwar hukumar tsaro da zata yi aiki wajen dakile yawaitar kashe-kashe da ‘yan fashin daji a jihar.
Sabuwar hukumar tsaron wanda ake kira ‘Community Protection Guards (CPG)’ kwatankwacin kungiyar tsaro ta Yammacin Nijeriya, wacce aka fi sani da Amotekun, wacce ta fara aiki a watan Janairun 2020.
- ‘Yan Bindiga Sun Tashi Garuruwa 30 A Zamfara Da Bayar Da Umarnin Tashin Wasu 5 A Jihar Filato
- A Dau Bindiga: Babu Hukuma A Zamfara?
An fara horar da kashin farko na mutum 500, wadanda aka dauka daga dukkan masarautu 19 da ke jihar.
Gwamna Bello Matawalle ya kaddamar da horon a ranar Asabar a Gusau.
Matawalle ya ce gwamnatin jihar Zamfara ta fara daukar sabbin matakan tsaro, ya ce masu Jami’a za su dauki makamai yayin gabatar da aikinsu.
Gwamnan ya ce, an yanke shawarar kafa jami’an kare hakkin jama’ar ne saboda burin gwamnatinsa na samar da duk hanyoyin da za a bi don magance karuwar ayyukan ‘yan fashi da ke haddasa asarar rayuka da wahalhalun da ba a taba gani ba da kuma wargaza zaman lafiya a wasu sassan jihar.
Matawalle ya shaidawa Jami’an Tsaron Al’uma aikin da ke gabansu, sannan ya bukace su da su mayar da hankali sosai kan horar da suke samu.
Matawalle ya tabbatar da cewa, a karshen wannan horon, za a tura mambobin CPG zuwa yankunansu daban-daban na masarautun jihar 19, domin baiwa jami’an tsaro kwarin gwiwa wajen yaki da ‘yan fashi da miyagun laifuka.
Elkana yayin da yake bayyana cikakken goyon bayan rundunar ga Gwamna Matawalle a yakin da ake yi da ‘yan fashi, ya bukaci masu daukar ma’aikata da su kasance masu bin doka da oda, masu tsoron Allah, kuma masu kishin kasa wajen gudanar da ayyukansu domin cimma burin da ake so.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Rtd DIG Mamman Ibrahim Tsafe ya ce an kafa jami’an kare hakkin jama’a ne da nufin taimakawa jami’an tsaro wajen ganin an tabbatar da tsaro a jihar daga dukkan munanan laifuka a duk sassan jihar.
Taron ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya da sakataren gwamnatin jiha Alhaji Kabiru Balarabe.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Gusau, Malam Ibrahim Suleiman, shugaban ma’aikata na jiha, Alhaji Kabiru Muhammad Gayari, ‘yan majalisar zartarwa na jiha da shugabannin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar, suma sun halarci taron kaddamar da shirin horaswar.