Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris ta samu goyon baya mai rinjaye na wakilan jam’iyyar Democrat domin kasancewa ‘yar takarar shugabancin kasar a jam’iyyar.
Wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya yi ya nuna cewa Kamala ta samu goyon baya daga wakilan jami’iyyar fiye da 1,976 da take bukata ta samu nasarar zama ‘yar takarar jam’iyyar a zagayen farko na zaben.
- Za A Ci Gaba Da Daukar Shirin ‘The Mandate’ A Kasar Faransa – Ezinne Agwu
- Kamfe: An Tara Wa Kamala Haris Kusan Dala Miliyan 50 Cikin Sa’o’i 2 A Amurka
Hakan kuwa na nufin Misis Harris na dab da zama ‘yar takarar shugabancin kasar ta jam’iyyar ta Democrat domin karawa da dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump a babban zaben na watan Nuwamba.
Sai dai hakan zai zama a hukumance ne kawai lokacin da wakilan jam’iyyar da za su zaben suka kada kuri’a a babban taron jam’iyyar a Chikago a wata mai kamawa.
Wakilan dai su ne mutanen da ke wakiltar mazabunsu. Kuma alkawarin goyon bayan da suka sanar bai zama wajibi su bi ba har sai lokacin kada kuri’a duk da dai da wuya hakan ya sauya.
har yanzu dai babu wani da ya fito a bayyane ya kalubalanci Misis Harris tun bayan da shugaba Joe Biden ya sanar da ficewa daga takarar ranar Lahadi.
Ya fuskanci matsin lamba daga jiga-jigan jam’iyyar ta Democrat sakamakon rashin katabus a mahawarar da ya yi da Mista Trump.
Idan dai har irin goyon bayan da take samu zai zama kuri’a a lokacin taron jam’iyyar Democrat da za a yi tsakanin ranar 1 zuwa 7 ga watan Agustan 2024, to Misis Harris za ta zamo ‘yar takarar jam’iyyar.
Binciken na AP na nuni da irin girman goyon bayan da Kamala Harris ke samu tun bayan da Joe Biden ya sanar da ajiye takarar tasa.
Har wayau wani abu shi ne yadda aka tara wa Kamala Harris tallafin miliyoyin Daloli tun bayan sanarwar ficewar ta Mista Biden sanna kuma jiga-jigan jam’iyyar ta Democrat sun shirya goya mata baya.
Ana sa ran Misis Harris za ta bayyana a wani gangamin magoya baya a Milwaukee da ke Jihar Winsconsin ranar Talata kuma wanda shi ne zai zama gangaminta na farko tun bayan da Mista Biden ya fice daga takarar kuma ya goyi bayan mataimakiyar tasa.
A wani bangaren kuma Mista Biden zai koma fadar White House bayan kwashe dan wani lokaci sakamakon kamuwa da cutar Korona. Mista Biden zai gana da firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a wannan makon a yayin ziyarar da Netanyahun zai kai Washinton.
Da take jawabi ga ma’aikata a ofishin kamfe dinta a Wimington a Jihar Delaware Misis Harris alamu sun nuna ta shirya wa Mista Trump.
Da take bayyana kanta a matsayin mai shari’ar da ta hukunta masu laifi, sai ta kara da cewa: “Na san irin su Donald Trump.”
Ta kara da cewa takarar Biden da Harris ta zamo wani da ke alamta kishin makomar Amurka da tasu da kuma ta Donald Trump.
“Wani yana duba gaba, dayan kuma yana waiwayen baya,” Harris ta ce. “Donald Trump yana son komar da kasarmu baya mu kuma mun yi imani da makoma mai kyau da za ta yi kyau ga dukkannin Amurkawa.”
Ta kuma yi nuni da irin nasarorin da Mista Biden ya samu, tana mai cewa aikin da ta yi tare da shi a matsayinta na mataimakiyar shugaban kasa “shi ne wani abun da cimma babba a rayuwarta”.
kafin dai Misis Harris ta hau dandamalin kmafe ta fara magana, sai da mista Biden ya fara yin tsokaci ta wayar tarho a wani yanayi na farko tun bayan sanarwar da ya yi na ficewa daga takarar bayan kamuwa da cutar korona.
Ya fara ne da yin godiya ga masu taimaka masa inda ya nemi da su “rungumi” Misis Harris saboda “ita ce ta fi dacewa”.
“Na san cewa labarin da kuka ji jiya ya girgiza ku to sai dai abin da ya fi dacewa a yi kenan,” In ji Mista Biden.
Ya kuma sha lawashin shiga gangamin nema mata kuri’a kan-jiki-kankarfi kasancewar yadda mulkin demokradiyya ke fuskantar barazana.
Shi kuma mataimakin Donald Trumpna jam’iyyar Republican, Sanata JD Bance, ya soki Misis Harris da Mista Biden baki dayansu a lokacin yakin neman zabe a Birginia.
“Tarihi zai rinka tuna wa da Joe Biden ba kawai a matsayin dan takarar da ya gudu ya bar ladansa ba, har ma da kasancewarsa shugaban Amurka da ya fi kowane lalacewa,” in ji shi.