Gwamna Darius Dickson Ishaku na Jihar Taraba, ya nemi afuwar mutanen Taraba wadanda gwamnatinsa ta yi wa ba daidai ba na shekaru takwas.
Ishaku ya nemi gafarar ne a yayin taron godiya da kungiyar kiristoci ta kasa reshen Jihar Taraba ta shirya a sakatariyar CAN da ke Jalingo.
- Yau Tinubu Zai Dawo Nijeriya Bayan Ya Shafe Kwanaki 34 Baya Kasa
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 63, Sun Ceto Mutum 150 Da Aka Sace
Gwamnan ya ce ya yi farin ciki da yadda littafinsa na “Ba Ni Zaman Lafiya Zan Baku Ci Gaba” ya samu gindin zama a zukatan ’yan Taraba, inda ya bukaci jama’a da su bar ruhin zaman lafiya da soyayya da gafara ya jagoranci halayensu da ayyukansu.
Ishaku dai ya yi godiyar Easter a Cocin Anglican Mayo Dasa da ke Jalingo, babban birnin jihar babban birnin Jihar.
“A matsayina na shugaban da ya jagoranci jihar nan kusan shekaru takwas, mai yiwuwa na yi wa mutane da yawa laifi ko dai da sanina ko kuma cikin rashin sani a dalilin gudanar da ayyuka a matsayina na Gwamna,” in ji shi.
Ishaku ya bayyana cewa Littafi Mai Tsarki ya ce ya fito fili ya nemi gafarar wadanda watakila ya yi wa laifi.
“A cikin Littafi Mai Tsarki, an koya mana mu gafarta wa wadanda suka yi mana laifi. A wannan yanayin, ina rokon wadanda na yi wa laifi su gafarta min. Na yi haka ne a dakin Allah, idan kuma ba su yafe min ba, tsakanin su da Allah ne,” in ji shi.
Gwamnan mai barin gado ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya ba shi hikimar yi wa al’ummar jihar hidima yadda ya kamata duk da kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta.
Sai dai ya bukaci al’ummar jihar da su bai wa magajinsa Laftanar Kanar Kefas Agbu (mai ritaya) goyon baya da hadin kai domin samun nasara.
Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnan zai je gaban taron jama’a domin neman gafarar ‘yan siyasa da al’ummar Taraba a bainar jama’a kan batutuwa da wuraren da ya bata musu rai.
A makon da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma roki ‘yan Nijeriya da ya yi wa laifi su yafe masa.
Mako guda kafin Buhari ya nemi yafiar jama’a, Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, ya nemi jama’a su gafarta masa.