Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya iso Abuja, babban birnin tarayya, a yau Litinin.
Jirgin Tinubu ya sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, kuma ya samu tarba daga dimbin magoya bayansa.
- Kamar Buhari Da Ganduje: Darius Ishaku Ya Nemi Gafarar ‘Yan Taraba
- Kamfanin Jiragen Air Peace Zai Dawo Da ‘Yan Nijeriya Gida Daga Sudan Kyauta
Zababben shugaban kasar, ya zo ne daga kasar Faransa tare da uwargidansa Oluremi Tinubu, a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, inda suka samu tarba daga mabiya jam’iyyar APC da magoya bayansa da suka yi ta hasashen zuwansa.
Talla
Tun da fari Tinubu ya shafe sama da wata guda baya Nijeriya.
Jam’iyyar APC ta ba da sanarwar sabon zababben shugaban kasar, zai dawo gida Nijeriya a yau Litinin.
Talla