A ranar Asabar 12 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta gabatar da takardar bayani kan kayayyakin da za ta soke wa harajin kwastam na yin-min-na-maka da ta kara kakkabawa masu sassa, ciki hadda na’urorin kwamfuta da wayar salula, da na’urorin laturoni masu amfani da “Semiconductor”, da hadadden allon taswirar layukan wuta da dai sauran kayayyaki. Matakin da ya girgiza bangarorin daban-daban.
A daren jiya kuma, Sin ta bayyana wannan mataki a matsayin karamin kokari da Amurka ta yi na daidaita kuskurenta na kakabawa sauran sassa harajin kwastam na yin-min-na-rama.
Alal hakika, dole ne gwamnatin Amurka ta dauki wannan mataki, duba da matsayinta na kasa ta biyu a duniya a bangaren fitar da kayayyakin da ba a kammala sarrafa su ba, inda kayayyakin zamani da Amurka ke samarwa ke dogaro da karfin kasashe masu tasowa, da saurin bunkasuwa ciki har da kasar Sin, wadanda ke da fifiko ta fuskar samar da kayayyaki, da karfin dunkulewar sana’o’i. Amurka ta kambama kanta game da sana’o’inta, ta kuma kaskantar da matsayin da ake ciki na cewa, tsare-tsaren samar da kayayyaki a duniya na dogaro ne da juna, ta yadda ba za a iya raba bangarorin biyu ba.
Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na shiga gogayyar ciniki.
Bisa bayyanan da aka fitar, Amurka ta dade tana cin rarar kudin ciniki a bangaren ba da hidimomi. Alal misali a shekarar 2024, yawan rarar kudin da ta samu a wannan bangare ya kai dala biliyan 300. Kuma Abin lura shi ne, cinikin hidimomi na matukar dogaro da cinikin kayayyaki. Gibin kudin cinikin da Amurka ta samu a bangaren cinikin kayayyaki da rarar kudin cinikin da ta samu ta fuskar cinikin hidimomi, ya faru ne bayan sauyin salon sana’o’i bisa matakai daban daban, ta yadda suka kasance tagwaye da ba za a iya raba su ba.
Idan an yi waiwaye kan tushen cinikin hidimomi wato batun amincewa, a wadannan shekaru da suka gabata, Amurka ta rika sanya takunkumai da haifar da barazana ga dukkanin fadin duniya, wanda hakan ya rage kimarta, da amincewa daga sauran kasashe. A halin yanzu, Amurka ta kakabawa sauran kasashe harajin kwastam yadda take so, kuma abun tambaya shi ne wa zai karbi hidimomin da Amurka za ta samar a bangaren hada-hadar kudi, da ba da ilmi da bayanai da kuma kwamfuta?
Amurka ita kanta za ta dau laifin gogayyar ciniki, matakin da ta dauka a wannan karo na kawar da harajin kwastam na ramuwar gayya kan wasu kayayyaki, dabara ce ta kubutar da kanta daga mawuyacin hali. Amma, hakan bai wadatar ba, dole ne ta dauki karin matakai na soke dukkanin wannan haraji da ta kakabawa sauran kasashe. A wani bangare kuwa, ta mutunta abokan cinikinta, ta yi shawarwari da su bisa adalci da daidaito, a matsayin hanya daya tilo mafi dacewa da za ta bi wajen warware bambancin ra’ayi na ciniki. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp