Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa, daliban da yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ya shafa, ya kawo wa karatunsu tsaiko, kamta ya yi su kai kungiyar kara kotu su nemi diyyar bata musu lokacin karatunsu.
Ministan ya bayyana haka a wani jawabinsa yana me neman a biyan diyya ga daliban da yajin aikin na ASUU ya gurgunta wa harkokin karatunsu.
- Tsarin Ba-aiki-ba-biyan Albashi Ya Jinkirta Sulhunta Yajin Aikin ASUU – Adamu
- Yajin Aikin ASUU: Gwamnatin Tarayya Da ASUU Sun Tashi Daga Tattaunawa Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba
Adamu, ya ce alhakin ASUU ne ta biya daliban diyya tunda kungiyar ce ta rufe Jami’o’i ba gwamnati ba.
Ministan ya bayyana haka a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis, a lokacin da yake karin haske dangane da batun sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar.
Ministan ya ce aiwatar da tsarin Gwamnatin Tarayya na ba-aiki-ba-biya ne kadai ke kawo tsaiko wajen yin sulhu da kungiyar.