Kamfani BYD na kasar Sin dake zaman jagora a bangaren kera motoci masu amfani da lantarki, ya ba da rahoton samun riba mai gwabi a shekarar 2024, biyo bayan ciniki mai yawa na sayar da motoci.
Cikin rahotonsa na shekara-shekara da aka mikawa kasuwar hannayen jari ta Shenzhen, kamfanin ya ce, ribar da masu hannun jari a kamfanin suka samu ya karu da kaso 34 kan na shekarar 2023, zuwa yaun biliyan 40.25, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 5.6.
- Ministan Lafiya Ya Yi Alƙawarin Inganta Tallafi Ga Likitoci A Hajjin 2025
- SDP: Ba Mu Yi Wa Kowa Alƙawarin Takarar Shugaban Ƙasa Ba
A bara, kamfanin ya samu kudin shigar da ya kai yuan biliyan 777.1, karuwar kaso 29.02 a kan na shekarar 2023 da ta gabace ta.
Kamfanin na BYD na ci gaba da samun tagomashi wajen sayar da motoci. A bara, ya sayar da motoci masu amfani da lantarki miliyan 4.27, karuwar kaso 41 kan na shekarar 2023. Kana yawan motocin da ya sayar a ketare, ya kai 417,000, adadin da ya karu da kaso 72.
Har ila yau a baran, kudin da kamfanin ya kashe kan ayyukan bincike da samar da motoci, ya karu da kaso 36 kan na shekarar 2023 da ta wuce zuwa yuan biliyan 54.2, adadin da ya kai jimilar kudin da ya kashe a bangaren, ya zarce yuan biliyan 180. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp