Kamfanin Meta wanda shi ne mallakin Facebook da Instagram, ya kaddamar da manhajar sabon shafinsa na sada zumunta da muhawara, mai suna ‘Threads’ a matsayin kishiya ga Twitter.
Shafin na Threads, yana dauke da abubuwa kamar yadda Twitter yake kuma wanda yake da shafin Instagram zai iya samunsa ta wannan shafin cikin sauki.
- Bincikenmu Ya Nuna Bidiyon Dalar Ganduje Gaskiya Ne –Muhyi
- SCO Ta Ba Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Tsaro, Da Sauye-sauye Na Zamani
‘Yan sa’o’i da kaddamar da shi shafin har ya samu sama da mutum miliyan 10 da suka yi rajista da shi.
Ba ma ga kwararru ba da suka kalli kaddamar da wannan sabon shafi ko manhaja ta Threads a matsayin kishiya ga Twitter mallakar Elon Musk, Mark Zuckerberg mai katafaren kamfanin Meta da ya mallaki Facebook da Istagram ya furta da kansa cewa Threads wanda ya kunshi abubuwa da ke kusan irin na Twitter zai kasance kishiya da nufin zarce Twitter.
Tuni miliyoyin mutane suka shiga fara amfani da Thread.
Hakan ya sanya babu wani batu da ake tattaunawa a kafafen sada zumunta face zancen Thread.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp