A shekara ta 2024, kamfanin harhada magunguna na Denmark, wato kamfanin Novo Nordisk ya sanar da zuba jarin kusan Yuan biliyan 4, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 557 a birnin Tianjin na Sin. A watan Yulin bana kuma, kamfanin ya sake sanar da zuba karin jari na kusan Yuan biliyan 0.8, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 11 don fadada dakin gwaje-gwajen ingancin kayayyaki a masana’antarsa ta Tianjin.
Shugaban hukumar zartaswa ta Novo Nordisk Helge Lund ya bayyana cewa, fagen nazari da yaki da cututtuka na yau da kullum a Sin, ya zama wata dama ta kasuwanci, kuma dakile wadannan cututtuka, nauyi ne dake wuyan Novo Nordisk. Ya ce kamfanin yana matukar yaba wa gwamnatin Sin saboda manufofi da ayyuka masu karfi da ta gudanar game da yaki da cututtuka na yau da kullum.
A matsayin abokiyar hulda ta dogon lokaci, Helge Lund ya bayyana cewa, Novo Nordisk na fatan ci gaba da ba da gudummawa ga yaki da cututtuka na yau da kullun. Kuma yayin da Sin ke ci gaba da gina wayewar kai ta zamani, kamfanin zai ci gaba da kara zurfafa shiga kasuwar Sin ta hanyar kirkire-kirkire da hadin gwiwa, domin cimma buri na moriyar juan da kuma samun riba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp