An yi bikin kaddamar da aikin gina hanyar motoci masu saurin tafiya ta farko a Abidjan, fadar mulkin Cote Di’voire a ran 10 ga wata, wanda wani kamfanin Sin zai taimaka wajen gina shi.
Firaministan kasar Robert Beugré Mambé ya bayyana cewa, wannan hanya za ta amfanawa al’ummar kasar a bangaren zirga-zirga, kuma za ta daga ingancin zaman rayuwarsu. Yana mai cewa, mazauna birnin na matukar bukatar wannan hanya, shi ya sa gwamnatin kasar da jama’arta ke daukar ta da muhimmanci matuka.
An ce, za a yi wannan hanya a birnin Abidjan fadar mulkin kasar, wadda tsawonta zai kai kilomita 20, da tasoshi na zamani 21, kuma za ta ratsa yankin Yopougon da ta hada Abidjan da Bingerville, aikin zai kuma samar da guraben aikin yi kimanin 500 kai tsaye. (Amina Xu)