Kamfanin gine-gine na kasar Sin wato CRJE mai ayyuka a gabashin Afirka, ya kammala aikin ginin babbar cibiyar horarwa ta hidimomin yawon bude ido da karbar baki a birnin Jinja na gabashin kasar Uganda.
Ginin cibiyar na zamani mallakin gwamnatin kasar, na kunshe da otal da kuma cibiyar samar da kwararrun ma’aikata. Hakan na zuwa ne yayin da Uganda ke kokarin bunkasa samar da kudaden shiga ta hanyar amfani da kwararrun ma’aikata.
- Tsohon Shugaban NNPC, Kyari Ya Musanta Zargin Faɗawa Tarkon EFCC
- Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025
Da yake tabbatar da hakan, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai a ranar Juma’a, mataimakin shugaban sabuwar cibiyar Moses Kaneene, ya ce ginin ya kunshi ofisoshin ayyukan gudanarwa, da ajujuwan dalibai, da babban dakin gudanar da taruka.
Kaneene, ya ce ginin na kunshe da dukkanin kayayyakin aiki da ake bukata, ciki har da dakunan kwamfuta, da na gwaje-gwaje, da dakin dafa abinci. Ya ce “Ba yadda za a iya samar da kwararrun ma’aikata ba tare da kayan aiki ba. Samar da cibiyar aiki ta zamani, zai taimaka wajen kyankyashe jami’ai masu sanin makamar aiki da ake bukata domin cimma nasarar bunkasa sashen yawon bude ido.”
Ya ce, sabanin yadda lamarin yake a baya, lokacin da ake da karancin kayayyakin aiki, inda ake horar da dalibai 400 kacal, a yanzu cibiyar na iya horar da dalibai har sama da 1,000. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp