A ranar Juma’ar makon jiya ne Jakadan kasar Indiya a Nijeriya Mista Gangadharan Balasubramanian ya bayyana cewa, zuwa yanzu kamfanonin kasar Indiya 150 suka samu nasarar zuba jarin fiye da Dala Biliyan 27 a sassan tattalin arzikin Nijeriya daban-daban.
Jakadan ya bayyana haka ne a taron bikin cikar kasar Indiya shekara 75 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
- Kamfanonin Ketare Dake Kasar Sin Sun Amince Da Makomar Tattalin Arzikinta
- Karancin Gas Ya Jefa Al’umma Cikin Duhu Da Matsaloli A Bangaren Lantarki A Nijeriya
Ya kuma kara da cewa, dagantaka a tsakanin Nijeriya da kasar Indiya na da dadadden tarihi, tun kafin kasashen biyu su samu ‘yancin mulkin kai.
Ya ce, kyakywan dagantakar da ke tsakanin kasashen biyu ya sa Indiya ta gayyaci Nijeriya zuwa taron G20 a lokacin da Indiya ke shugabancin kungiyar.
“Cikin alkawarin jarin naira biliyan 14 da aka yi a lokacin ziyarar a halin yanzu an samu nasarar zuba jarin fiye da Dala Biliyan 7 a tattalin arzikn Nijeriya.
A nasa jawabin, ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce, Nijeriya da Indiya na da dangantaka mai tsawon tarihi, suna kuma aiki tare har a majalisar dinkin duniya.