Yana daga cikin abunda zai nuna maka kamshin Annabi da duk abin da ya fita a jikinsa, shan jinin Annabi da Imam Malik bin Sinanin, Abi Kudri ya yi a ranar yakin Uhudu. Sannan kuma Annabi ya yi mai bushara da cewa wuta ba za ta ci shi ba.
Irin wannan Hadisi ya faru da Zubairu bin Awwam, mijin Asma’u ‘yar Sayyidina Abubakar uwar Abdullahi bin Zubair dan da aka fara haifa a Madina bayan Hijra.
- Mawakiyar Yabon Fiyayyen Halitta Annabi (SAW), Rukayat Gawat Ta Rasu
- Karin Harajin Amurka Ba Zai Dakile Sashen Kere-Keren Kasar Sin Ba
Wata rana Zubairu bin Awam ya yi wa Annabi Muhammad (SAW) kaho, sai Annabi ya yi masa umarni da ya je ya zubar da jinin, bayan ya je zubarwa sai ya shanye jinin, da ya dawo sai Annabi ya fahimci hakan a fuskarshi, sai ya ce masa ka sha jinina? sai Annabi ya ce masa “Wailul laka minannasi, wa wailul lahum minka – kaicon ka da mutane kuma su ma kaicon su da kai”. Annanbi (SAW) bai yi inkarin shan jininsa ba.
An sake ruwaito irin wannan hadisi a cikin (sha’anin) wata mata, wacce ta sha fitsarinsa (SAW), ita ce Barakatu ko Ummu Aimana, Annabi (SAW) ya ce mata kika sha Fitsari na! ba za ki kara ciwon ciki ba.
Amma Annabi (SAW) bai taba umartar daya daga cikin wadanda suka sha jininsa ko fitsarin sa da wankewa ko kuskure baki ba sannan kuma bai taba ce musu kar su kara ba. Hadisin wadanda suka sha jinin Annabi ingantacce ne duk a wurin Malamai.
Hadisin wannan mata mai shan fitsarin Annabi an yi sabani a cikin wacce ta sha fitsarin, wasu sun tafi cewa Ummu Aimana ce wacce ta raini Annabi wasu kuma sun tafi a kan ‘yar dakin ‘yar Abu Sufyan ce Matar Annabi, kadimar Annabi (SAW). Yadda abin yake shi ne akwai wani sassaken Dabino da aka yi shi kamar akushi ana shigar da shi inda Annabi yake da dare don yin fitsari a cikinsa, ana ajiye shi a karkashin gado, wata rana sai wannan mata ta tashi tana jin kishin ruwa, garin lalube sai ta ga wannan abu da ruwa mai aminci a cikinshi, sai tasha, da safe Annabi ya ce a fitar da fitsari, sai wannan mata ta ce “ya Rasulullahi na tashi cikin dare ni kuma ina jin kishin ruwa, ina neman ruwa sai na ga wannan ni kuma sai na shanye, ni kuma ban san meye ba.” Ibn Juraidu da sauran Malamai duk sun ruwaito wannan Hadisi.
Manzon Allah (SAW), an haife shi da Kaciyarshi kuma abun yanke wa Cibiya, in ji Shaffa’u.
An karbo daga Mahaifiyarsa, Aminatu (RA) ta ce na haife shi tsarkakakke ba shi da wata kazanta. Kuma an karba daga Sayyada A’isha Ummul Muminina tana cewa ban taba ganin tsiraicin Annabi (SAW) ba.
An karba daga Sayyidina Ali Karramalahu wajhahu yana cewa Annabi Muhammad (SAW) ya yi mun wasiyya yana mai cewa “Kar in bar wani ya yi mai wanka sai ni” sabida Annabi ya ce min “babu wanda zai ga Al’aurata face an shafe idanuwansa”, ma’ana karshen rayuwa zai makance kamar yadda duk wadanda suka ga Mala’ika Jibrilu su ma akarshen rayuwa sun makance.
An karbo daga Hadisin Ikrama cewa wata rana Annabi ya yi bacci, har ana jin minsharinsa, da aka kira Sallah sai ya tashi ya yi Sallah bai yi Alwala ba, sai Ikrima ya ce “Shi Annabi Muhammad (SAW) ya kasanace abin kiyayewa ne ko bacci yake ya san abin da ke faruwa”.
Yanzu kuma a wannan zango za mu yi magana a kan cikar Hankalinsa da Fasahar harshensa (SAW).
Cikar hankalin Annabi: Idan muka yi duba zuwa ga cikar hankalinsa da kaifin fahimtarsa da karfin masu riskarsa (Abu biyar) da fasahar harshensa da daidaiton motsinsa (ba bazo-bazo ko kasalanci) da kyawawan dabi’unsa babu kokonto, Annabi ya kasance mafi hankalin mutane kuma mafi kaifin fahimtarsu, musamman idan aka yi la’akari da yadda Annabi yake shirya abubuwan boye na halitta – abun da zuciyarsu ta shiryu da shi, da yadda ya shirya musu lamarin bayyanensu – Lamarin yadda suke gudanar da rayuwa ta yau da kullum da yadda ya shirya abubuwan da za su amfani sauran halitta da yadda ya shirya wa kebantattu tsarin rayuwarsu tare da ban mamakin dabi’unsa da kayatarwa a tarihinsa, balle kuma mutum ya duba abubuwan da ya kwaranyo na Ilimi sannan ya tabbatar na daga Shari’a ba tare da ya koya daga kowa ba ko a ce an yi gogayya ko ya karanta a littattafan da suka gabata, duk ba a yi wannan ba, daga Allah yake.
Malam Wahabu, masanin ilimin Yahudu da Nasara sannan ya kara da na Musulunci ya fada yana cewa “Na karanta littattafai Saba’in da daya na Yahudu da Nasara sai na samu a cikin dukkan wannan littattafai, cewa lallai Annabi Muhammadu (SAW) shi ne mafi rinjayen mutane a hankali kuma shine mafificinsu wajen ra’ayi.
A cikin wata ruwaya ta wannan malami, ya ce “Sai na samu a cikin dukkan wadannan littattafai da aka saukar wa Annabawa cewa lallai Allah bai ba wa mutane tun daga farkon duniya har izuwa karshenta na daga hankali ba idan aka gwada da na Annabi Muhammad (SAW), face sai ka samu (tamkar) kwayar rairayi ce a cikin fadin duk yawan saharar duniya.”
Yana nufin, hankallin mutanen duniya daga farko izuwa karshe shi ne kwayar rairayin, na Annabi kuwa shi ne yawan fadin duk saharar Duniya.
Malam Mujahidu ya ce, Manzon Allah (SAW) ya kasance, idan ya tashi zai ja Sallah, yana ganin duk wadanda ke bayan shi kamar yadda yake ganin duk wanda yake gabanshi, da wannan magana ce malamai suka fassara ayar “Watakallubaka fis sajidin – da jujjuyawarka a cikin masu Sujada”
Ya zo a cikin Littafin Muwadda ta Imam Malik, daga Annabi (SAW) yana cewa “Ni ina ganinku ta bayana” an kuma karba irin wannan Hadisin daga Anas a cikin Bukhari da Muslim.
An karba daga Sayyada A’isha (RA) irin wannan Hadisin tana cewa “Meye abun mamaki don an ce Annabi yana gani ta baya, ai kari ne cikin Mu’ujizozinshi”
Annabi Muhammad (SAW) an dauko masa Sarkin Habasha, Najashi lokacin da ya rasu yana Habasha, Annabi Yana Madina amma yace da Sahabbai ku tashi mu yi Sallah, Najashi ya rasu. Sahabbai suka ce ba ma shakkar Najashi yana nan kwance a gaban Annabi. An kuma dauko masa Baitul Makdisi yayin da Kuraishawa suka nemi ya siffanta musu Masallacin kan batun Isra’i kuma an sake dauko masa Ka’aba lokacin da ya gina Masallacinsa a Madina, yayin kafa alkiblar masallacin, sannan malamai sun yi Hikaya cewa Annabi yana ganin duk Taurarin cikin Surayya guda 12. Duk wadannan abubuwan da muka lissafa na daga Sallar Najashi, Siffanta Baitul makdisi, aza alkiblar Masallacinsa zuwa Ka’aba, Ganin taurarin Surayya duk da idanunsa na ka guda biyu ya gansu, in ji Ahmadu bin Hambali da waninsa.
Abi Huraira ya karbo Hadisi daga Annabi (SAW), ya ce yayin da Allah ya yi Tajalli (Bayyana) ga Annabi Musa (AS), tun daga nan Annabi Musa (AS) ya fara ganin kiyashi a kan babban dutse mai nisan tafiyan mil 30 a cikin dare mai duhu. In dai Annabi Musa (AS) Sabida ganin Tajallin Allah ya fara ganin irin wannan, to ina Annabi Muhammad (SAW) da ya ga “Min Ayati Rabbihil Kubra”, ta yaya zai zama abin kuskure kan cewa Annabi yana gani ta bayansa kamar yadda yake gani ta gabansa.
Hakika labarai sun zo cewa Annabi Muhammad (SAW) ya kada Rukanata, wanda Rukanata shi ne mafi karfin ‘yan zamaninsa. Yadda abin yake shi ne, wata rana Annabi Muhammad ya kira Rukanata da ya shiga Musulunci, sai Rukanata ya ce shi dan kokawa ne don haka sai an yi kokawa an kayar da shi zai amshi musulunci, sai Annabi ya amince da sharadin Rukanata, sai da aka kayar da Rukanata sau Uku, duk juyi yana cewa bai shirya ba amma a karshe ya amshi Musulunci.
Abi Hurairata yana cewa “Ban taba ganin wanda ya fi Annabi sauri da gaggawa ba cikin tafiyarsa, sai mun hada da sassarfa kana muke cimmasa”.
Yana daga cikin siffofin Annabi Muhammad (SAW) cewa dariyarsa, Murmushi ce sannan idan zai juya gaba daya yake juyawa, ba ya waige kuma in yana tafiya kamar ciccira yake yi kamar yana gangarowa daga tudu.