Kyaftin din Ingila Harry Kane ya koma Bayern Munich kan kwantiragin shekaru hudu, inda ya kawo karshen tarihinsa a Tottenham.
Dan wasan ya kulla yarjejeniyar sama da Yuro miliyan 110 (£95m) kuma zai iya buga wasansa na farko a wasan Super Cup na Jamus da RB Leipzig ranar Asabar.
- Da Dumi-Dumi: Bayern Munchen Ta Kulla Yarjejeniya Da Tottenham Domin Siyan Kane
- Kane Ya Zura Kwallaye 4 A Ragar Shaktar Yayin Da Bayern Ke Cigaba Da Nuna Sha’awar Daukar shi
Kane, mai shekaru 30, ya bar Spurs a matsayin wanda ya fi zura kwallaye a tarihinsu inda ya zura kwallaye 280 a wasanni 435 da ya buga.
A cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta ya ce yana jin cewa lokacin barinsa ne Spurs.
Ya lashe kyautar takalmin zinare na gasar Premier sau uku – a cikin 2015-16, 2016-17 da 2020-21 – kuma da kwallaye 213 a wasanni 320 a gasar Ingila,
Inda yake bukatar kwallaye 48 kawai don karya tarihin Alan Shearer a gasar Premier.
Kane shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga ga kasar Ingila inda ya zura kwallaye 58 a duniya, bai taba cin wani babban kofi da kulob ko kasa ba.