Kangin man fetur da aka fara fuskanta tun daga makon jiya wanda ya faro daga Abuja kana ya watsu a dukkanin fadin kasa, ya sake wujijjiga ‘Yan Nijeriya wadanda dama can suna cikin mawuyacin hali, tun daga lokacin da aka cire tallafin mai a watan Mayun 2023.
Matsalar karancin man ta kara ta’azzara ta yadda abin ya zama ana tsaka da kukan targade sai kuma ga karaya ta samu.
Kamar yadda rahotanni ke ci gaba da bayyanawa, matafiya da dama a sassan kasar daban-daban; sun makale a inda suke, sakamakon yadda farashin man fetur din ya ninku da fiye da kashi 50 cikin 100.
Har ila yau, lamarin ya kai ga mafi yawan masu motocin haya; sun hakura sun ajiye ababen hawansu, a gefe guda kuma ‘yan kasuwa da ma’aikata sun koma tafiya wuraren aiki da kafa.
Mutane daga bangarorin da dama, musamman talakawa masu neman abin kai wa bakin salati; na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu tare da kiraye-kiraye ga masu ruwa da tsaki su shawo kan wannan al’amari, sakamakon irin mummunan halin kunci da talaucin da suka kara shiga ciki.
Musabbabin Karancin Man Fetur
Wata majiya ta tabbatar da cewa, gwamnati na biyan kudin tallafin man fetur kimanin Naira tiriliyan 1.3 a duk wata, don kokarin ganin an ci gaba da samun man ba tare da farashinsa ya karu ko samun wata tangarda ga ‘yan Nijeriya ba.
Amma a makwanni uku da suka gabata; sai gwamnati ta dakatar da bayar da wannan tallafi bisa yakinin cewa, man fetur da ake da shi a kasa zai iya isar ‘yan Nijeriya har zuwa lokacin da Matatar Man Dangote; za ta fara fitar da nata man a watan Mayu mai zuwa, wanda suke da yakinin cewa; zai iya wadatar da ‘yan Nijeriya.
Har ila yau, masu rike da madafun iko na cikin matukar damuwa, ganin cewa abin da ake samu a matsayin riba na ci gaba da samun koma-baya ko tabarbarewa, don haka ya zama wajibi a yi wani abu a kai; wanda mafitar kadai ita ce, samar da man fetur din da za a rika amfani da shi a cikin gida Nijeriya.
Da yake tsokaci, mai magana da yawun Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Femi Soneye ya ce; “Ina nan a kan bakana, dangane da abin da na bayyana a ranar Alhamis (27 ga Afrilun 2024) cewa, duk yayin da aka samu akasi na rashin samun man fetur tsawon kwana biyu ko uku, dole sai matsalar ta ninku kafin abubuwan su dawo daidai kamar yadda suke.”
LEADERSHIP Hausa ta ji ta bakin masu iyali kan yadda karancin fetur din ya shafi rayuwarsu. Binta Bukar daga Jihar Kano; ta koka da rashin wadataccen abinci da sauran abubuwan masarufi da kuma yadda ita kanta rayuwar ta yi matukar tsada. “A halin yanzu ba kowane gida ne a kullum ke iya dora tukunya ba, wasu kawai sai dai su sha ruwa su zuba wa sarautar Allah ido.
“Ko shakka babu, mutane suna cikin masifa da zafi da kuma radadi na halin da ake ciki, wanda ko kadan ba zai taba misaltuwa ba, ana kuka musamman na rashin abinci a halin yanzu ga kuma tsadar abinci; ko me kika daga ya yi tsada.
Sannan, ina mai tabbatar miki da cewa, ba kowane gida ne ake iya cin abinci sau biyu ba, idan aka samu dan abin da aka lasa da safe; da rana kuwa sai dai kawai godiyar Allah. Idan kika dauki taliya wadda talaka zai ci ya dan ji dadi, Naira 750 ake sayar da kowace guda daya; idan mutum yana da yara da yawa guda nawa za a ci a gidansa tsakani da Allah?”, in ji ta.
Ta kara da cewa, “sannan ga abubuwa da dama a ce wannan a ce wancan, kazalika ga kuma mazan suna nema su sakar wa mata komai da komai; idan na ce komai da komai, ina nufin komai da kika sani na rayuwa da suka hada da ci, sha, tufafi, kudin makarantar yara na Boko da Islamiyya da sauran abubuwa na rayuwa.
“Don haka, komai da kika sani; sai dai kawai mu yi wa Allah godiya. Idan kuwa kika shiga kauyuka, zai yi wuya ki samu gidan da ake dora tukunya da rana; sai dai kawai da daddare, wannan ga masu hali ma kenan. Yanzu ko dawa da ake ganin ta kamar abar banza ta kai ana sayar da buhunta a kan Naira 46,000, yanzu haka ko gwangwanin manja Naira 300 yake,” a ta bakinta.
Binta ta kara da cewa, “Allah ya kawo mu wani lokaci wanda kwata-kwata masu kudi ba sa son taimaka wa talakawa mabukata, kadan ne daga cikinsu masu dan tausayi da imani. Su kuma masu mulki, sai tsinanniyar karya; suna cewa an kai magani asibiti, haihuwa kyauta ce, abubuwa sun sauko wallahi duk karya ce, yanzu ga man fetur ya sake tashi na ji ana cewa; Naira 1,200, don Allah yaya talaka zai yi, wallahi yanzu kin ga yarana lokacin Islamiya ya yi; amma ba ni da abin da zan ba su su ci kuma dole haka za su tafi.” Ta bayyana.
Yanayin Da Aka Shiga A Adamawa
Wannan matsala ta karancin man fetur a Jihar Adamawa, ta zo ne a daidai lokacin da jihar ta fada matsalar rashin wutar lantarki, sakamakon lalacewa tare da sace wasu daga cikin kayayyakin da wasu bata gari suka yi, wanda hakan ya sa aka shiga matsalar duhu har na tsawon mako guda; ga kuma tsananin zafi da ake fama da shi, babu wuta, babu ruwan sha, sannan kuma babu man fetur.
A tattaunawar da LEADERSHIP Hausa ta yi da Malam Dahiru Gurin ya bayyana cewa, “gaskiya ‘yan Nijeriya ko mutanen Arewa, musamman a Jihar Adamawa, muna cikin wani muwuyacin hali; dalili kuwa a halin yanzu mun kusa kwashe mako biyu ba tare da wutar lantarki ba.
“Yanzu haka, ruwan leda (Pure water) duk guda daya ya kai Naira 50, a wani wurin ma Naira 100; wanda ko shakka babu, wannan tsadar man fetur din ce ta kawo haka, yau da safe mun sayi litar mai a kan Naira 1200 a garin Yola. Saboda haka, abin ya zama sai dai kawai addu’a.
Har ila yau, ya ce kudin mota da injin nika da sauran na komai da komai ma ya karu, “ga kuma yanayin zafi da ake ciki; abubuwan duk sun taru sun yi yawa, kawai sai dai neman sauki daga wurin Allah,” in ji Gurin.
Shi ma Ibrahim Abubakar, ya ce, “ka duba fuskata yadda take hada gumi, bakin ciki goma da goma, ina da mara lafiya a FMC; kai wa da dawowa kawai da mota, sai da na sayi mai galan daya a kan Naira 5,500, wani lokacin sai ka saya a kan Naira 5,700.
“Sannan kuma wallahi a rana sai na yi sawu uku, ban da kudin magani, don haka; mutane na cikin wani yanayi, yanzu abinci da sauran kayan masa rufi ganin mai ya tsada duk sun tashi, a kan idona wannan tsadar rayuwar da takaici ya kashe wasu a asibiti.”
“Na ga yarinyar da Maciji ya sare ta, iyayenta ba su da karfi; wallahi yadda za a kawo yarinyar nan asibiti a kan lokaci ya gagara, a karshe an kawo ta bai wuce da minti 10 ba; rai ya yi halinsa, akwai wani dattijo kuma a wannan matsala ta mai kafin a samu abin da za a dauko shi; shi ma ya rasu, zama na a asibiti na kwana uku na ga abubuwa da dama”, a cewar ta Ibrahim.
Jigawa
Mafi yawan gidajen man da ke Dutse, babban birnin Jihar; a rufe suke, inda ‘yan bunburutu ke cin kasuwarsu; ta hanyar sayar da kowace lita daya a kan Naira 1,100, wasu ma suna sayarwa har sama da haka.
Wannan dalili ne yasa, magidanta da dama suka yanke shawarar ajiye ababen hawansu, suka koma tafiya da kafafuwansu.
Kaduna
Haka nan, Jihar Kaduna ita ma na fuskantar wannan matsala ta karancin man fetur, wanda hakan ya yi sanadiyyar rufewar gidajen mai da dama; a gefe guda kuma ya kawo wa harkokin kasuwancin tasgaro kamar yadda wasu daga cikin ‘yan a jihar suka bayyana.
Wakilanmu da ke sa ido kan wannan dambarwa na Jihar Kano, sun bayyana mana yadda wasu daga cikin gidajen mai; wadanda suka bude suke sayar da shi a kan kowace lita Naira 1,000 a halin yanzu.
Kazalika, su kuma ‘yan bunburutu na sayar da duk lita a kan Naira 1,500, inda hakan ya tilasta wa mutane da dama ajiye ababen hawansu a gidajensu tare da bin motocin haya.
Kano
Gidajen mai da dama a Jihar Kano, na rufe sakamakon wannan karanci na mai a ake fama da shi. kazalika, ana sayar da wannan mai a kan farashi daga Naira 860, 950 har zuwa 1000; kamar yadda wani wanda ya jima a layin man kafin ya samu ya bayyana.
Haka zalika, ‘yan bunburu su ma na nan suna cin karensu babu babbaka, domin kuwa kamar yadda wata majiya ta bayyana, suna sayar da duk galan guda a kan Naira 5,000 zuwa 6,000.
Sannan, mafiya yawan abubuwan hawa na masu haya; sun dauke kafa cak, matafiya kuma sun shiga halin-ha’ula’i; ta hanyar yin jigum-jigum.
Filato
A Jos, babban birnin Jihar Filato; nan ma mafi yawan gidajen mai a rufe suke, wadanda kuma suke sayar da man; babu abin da ake iya gani face dogon layi iya ganinka. Haka zalika, ana sayar da kowace lita a kan Naira 800 zuwa 900.
Legas
Haka nan, a Jihar Legas ana sayar da duk lita guda a kan Naira 760, amma kamar yadda rahotanni suka bayyana; gidajen mai na NNPC na sayar da kowace a kan Naira 580.
Yadda Matsalar Ta Mayar Da Hannun Agogo Baya A Kan Iyakokin Kasar Nan
Katsina
Babu shakka, wannan matsala ta man fetur ta mayar da hannun agogo baya a Jihar Katsina da wasu garuruwa na kan iyakan Nijeriya da Nijar, domin kuwa ta haifar da gagarumar matsala ta bangarori da dama; musamman a bangaren da ya shafi tsadar kayayyakin abinci da sauran makamantansu.
A cikin garin Katsina, abin ya fara ne a hankali; daga baya kuma sai al’amarin ya zama tamkar wata annoba. Lokaci guda ne, aka wayi gari masu gidajen mai suka fara rufewa; wanda hakan ke nuna cewa, lallai matsala na nan tafe a wannan bangare na man fetur, kafin kace kwabo kuwa; lamarin ya fara cabewa a cikin kwaryar Katsina, inda aka rika yin dogon layi tare da kara farashin man fetur din daga Naira 700 zuwa 800 har kuma abin da ya yi sama, ya danganta da yadda ka samu man.
Batun shan man a gidan mai na NNPC kuwa, sai mai uwa a gindin murhu, domin kuwa su ne ke sayarwa a kan Naira 620 na farashin gwamnati, idan kuwa ba haka ba; kana iya yin kwana biyu ba ka sha man ba, saboda layi da kuma ‘yan cuwa-cuwa.
A cikin birnin Katsina, akwai wasu motoci kirar Passant da ke yin kaka-gida a gidajen man na NNPC, don shan man, sai dai bincike ya tabbatar da cewa; wadannan motoci na ‘yan bunburutu ne, ma’ana dai bayan sun sha man sai su koma gefe su karkatar da shi zuwa kasuwar bayan fage, don sayarwa da tsada.
Har ila yau, shiga cikin wannan hali; ya yi matukar canza al’amura a cikin dan kankanin lokaci, kayayyakin masarufi da kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi, tafiye-tafiye na neman gagarar jama’a, daliban na kasa zuwa makaranta ko zuwa a makare.
Yadda wannan matsala ta shafi matafiya kamar ya fi kowane bangare, domin kuwa yanzu an koma sai dai shiga motar gwamnati; saboda arharta ko kuma hakura da tafiyar in ba ta zama dole ba.
Jibiya Kan Iyakar Nijar Da Nijeriya:
Kamar yadda wannan wahala ta man fetur da tsada ta haifar da matsaloli da dama a Katsina, haka nan lamarin yake a garin Jibiya, mashahurin gari mai kasuwa wadda ta hada kan iyakokin Nijeriya da kuma Nijar, kamar yadda bayanai suka tabbatar; ana sayar da litar man fetur a kan Naira 1,500, sannan kuma ba kowane gidan man ba ne gwamnatin ta amince a sayar da man ba, tun lokacin da hukumar kwastan ta dakatar da wasu dillalan man fetur a lokacin Gwamnatin Muhammadu Buhari.
Wannan yanayi da aka shiga na wahala da karancin man fetur, ya taimaka wajan tsadar kayan abinci; musamman wadanda ake shigowa da su daga Kasar Nijar, haka nan kuma; ya takura wasu kananan ‘yan kasuwa da ke zuwa sayayya kasuwar ta jibiya daga Nijar da kuma wadanda ke zuwa Nijar din, domin sayo kaya.
Kamar yadda masana suka bayyana wannan matsala ta man fetur, ita kadai ce tilo wadda take game kowane irin al’amari a kasa cikin awa guda da zarar ta faru.
A Karamar Hukumar Kaita Da Dankama:
Haka nan, abin ya kasance a ranar Laraba a kasuwar Dankama; wanda ita ma mafiyawan wadanda suke cin kasuwar suna zuwa ne daga makwabciyar Kasar Nijar.
Kazalika, direbobi sun bayyana yadda irin wahalar man fetur din da kuma tsada ta tilasta musu rage yawan zirga-zirga, sakamakon wasu fasinjojin da suka saba zuwa kasuwa ba sa iya zuwa cin kasuwar.
“Yanayin kasuwar da gani ka san ya canza ba kamar yadda aka saba ba, duk da cewa yanzu kasuwar ana kawo dabbobi; wanda su ma sun kara kudi, sakamakon wannan matsala da ake fama da ita”, in ji direban.
A daidai lokacin hada wannan rahota, ana sayar da litar man fetur a kasuwar Dankama kan kudi Naira 1,400 zuwa 1,350, wanda hakan ya sa aka kara kudin mota da na daukar kaya.
A Karamar Hukumar Mai’aduwa
Ita wannan kasuwa ta kasance babbar kasuwa da ake tinkaho da ita a wadannan kasashe guda biyu, wato Nijeriya da kuma Nijar; sai dai kamar kowane gari su ma abin ya shafi yadda suke tafiyar da kasuwancinsu, sakamakon wannan tsada da wahalar da man fetur din ya yi.
A ranar lahadin da ta gabata, jama’a ba su cika kasuwar kamar yadda suka saba ba, hakan ya faru ne sakamakon yadda man fetur din ke wuta da kuma wahalar samu, duk da cewa ana zuwa daga jihohin kudancin wannan kasa, don cin wannan kasuwa.
Kasuwar Mai’a’duwa dai ta shahara wajen kawo dabbobi, wadanda suka hada da shanu, raguna, rakumi, jakuna, awaki da sauran makamantansu. Haka zaliak kuma, ana zuwa da mafi yawancinsu daga Nijar; musamman yanzu da aka bude kan iyakokin kasashen guda biyu, bayan tsawon lokacin da suka shafe a rufe.
Kamar yadda wani matashi ya shaida min ta wayar tarho, ya ce; duk abin da ka san farashinsa ya sauka saboda faduwar dala da saifa, yanzu ya koma yadda yake; sakamakon tashin farashin man fetur da kuma saifar, ya kara da cewa; yanzu muna cikin halin ga koshi ga kwanan yunwa, wato dai mun ga samu, mun kuma ga rashi.”
A bangaran hukumomi a Jihar Katsina kuwa, Mataimakin Gwamnan Jihar, Malam Faruk Lawal Jobe; ya shirya zama har sau biyu da mayan dillalan man fetur na jihar, domin tattaunawa da su kan yadda za a shawo kan wannan matsala, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto; ba ta sauya zani ba, domin kuwa ana nan ana ci gaba fama da wahalar wannan tsada ta man fetur a fadin jihar.
Kebbi
Haka zalika, Jihar Kebbi na daya daga cikin Jihohin Kasar Nijeriya da ke da iyaka da Kasar Jamhuriyar Nijar da kuma Benin, inda Kangiwa a yankin Arewacin Jihar ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar, sai kuma ta yammacin jihar da ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da kuma Benin.
Ko shakka babu, su ma wadannan yankuna; wannan tsadar mai da wahalar samun sa ta shafe su kai tsaye, musamman a bangaren da ya shafi harkokin kasuwancinsu na shige da fice a kan iyakokin yankunan. Har ila yau, ana zargin cewa; garuruwan da ke bakin wadannan iyakoki, ana ficewa da mai zuwa kasashen da suke makwabtaka da su, wanda ake ganin cewa; su ma sun taimaka wajen haifar da wannan matsala ta karancin man fetur a fdin wannan kasa.
Wakilinmu daga Birnin Kebbi, ya yi tattaki zuwa wadannan yankuna, na kan iyakokin Kangiwa da Kamba da ke jihar ta Kebbi, inda ya bayyana mana cewa; a bakin iyakar Kangiwa ana sayar da litar mai a kan Naira 1,000, ko 950 ko kuma 850 a gidajen mai, amma a kasuwar bayan fage; ‘yan buburutu na sayar da duk lita guda a kan Naira 1,200 zuwa 1,500.
Har ila yau, wani mutum da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, “akwai wani gidan mai a Kangiwa, wanda za a sayar da wannan mai; amma na ‘yan wasu sa’o’i kawai, sai kuma a rufe sai gobe. Amma cikin dare za su sake budewa, su sayar wa ‘yan kasuwar bayan fage, wadanda suke yin safararsa zuwa kasashen da suke makwabtaka da mu”, a cewar mutumin.
“Idan za ka iya fitowa tsakar dare, za ka tabbatar da abin da nake bayyana maka, musamman idan za ka tsaya a kan hanyoyin Baraya, Junju, Salwai, Balbal da kuma Bachaka; duk hanyoyi ne da ke zuwa Jamhuriyar Nijar, don safarar wannan mai na fetur,” daga wata majiya mai karfi.
A cewarsa, “shin abin tambaya a nan shi ne, babu ma’aikata ne ko kuwa ba sa yin aikinsu ne; wanda a duk wata ake biyansu, ake kwashe wannan mai ana ficewa da shi zuwa kasashen da muke makwabtaka da su?”
Haka zalika, a iyakar Kamba; nan ma duk kanwar ja ce, domin kuwa a nan ma ana yin safarar wannan mai na fetur zuwa Jamhuriyar Benin ta hanyoyin Dole-kaina, Buma, Tungar sule da sauransu ta barauniyar hanya, wadda jama’a ba su gano ba. Haka nan, a garin Kamba ana sayar da man a kan Naira 1000, 950, 1,200, har zuwa 1,500, amma duk da hakan ana ficewa da shi zuwa kasashen da muke makwabtaka da su.
Bisa binciken da wakilinmu ya gudanar, kasuwanci a yankunan ya yi matukar raguwa; haka nan kuma su ma kayayyakin sun kara tsada, saboda karancin samun man fetur din da kuma tsadarsa a yankunan. Sannan kuma, al’ummar da ke zaune a wadannan yankuna; na gudanar da rayuwarsu a cikin kunci da wahalar gaske.
Bayanan Masu Ruwa Da Tsaki
Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa, Reshen Jihar Katsina, (IPMAN) Alhaji Abbas Hamza ya bayyana wa manema labarai cewa, matsaloli ne guda biyu suka haifar da wannan tirka-tirka.
A cewarsa, cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi shi ne babbar sila, domin akwai kudaden da mambobinsu ke bin gwamnati na dako, wanda har yanzu ba a biya su ba; saboda haka, wasu ba za su iya ci gaba da yin wannan sana’a ba. Sannan, abu na biyu shi ne; yadda a watan Maris kwata-kwata ba a shigo da man fetur zuwa wannan kasa daga kasashen waje kamar yadda aka saba da yawa ba.
Har ila yau, akwai kuma wata sabuwar matsala da ta sake kunno kai ta barazanar da Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta yi cewa, idan har gwamnatin tarayya ba ta biya su bashin da suke bi na Naira biliyan 200 ba; za ta tsayar da dukkanin harkokin samar da wannan mai a fadin wannan kasa.
Idan har wannan barazana da kungiyar ta yi ta tabbata, babu shakka; ‘yan Nijeriya za suke fadawa cikin wani mawuyacin hali, baya ga wanda suke ciki a; suke kuma kan kokawa a kai a halin yanzu.
A bangare guda kuma, an jiyo Majalisar Wakilan Kasar nan ta gayyaci Karamin Ministan Harkokin Man Fetur, Heineken Lokpobiri da takwaransa mai kula da Iskar Gas, Ekperikpe Ekpo game da wannan matsala ta karancin mai da ake fama da ita a fadin wannan kasa.
Hakan kuwa, ya biyo bayan wani kudiri ne da Dan Majalisa, Umar Ajilo ya gabatar, inda ya bayyana damuwarsa game da ci gaba da ake samu na layuka a gidajen man da ke fadin Nijeriya baki-daya.
Haka zalika, Majalisar ta gayyaci Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari; a kan wannan matsala ta karancin man fetur.
Majalisar na sa ran Ministocin da kuma Shugaban Kamfanin Man Fetur din, za su yi mata bayani a kan musabbabin da ya haddasa karancin man da kuma matakan da za a dauka, domin shawo kan wannan al’amari.
Wakazalika, lokacin da ake kammala rubuta wannan rahoto, wakilinmu da ke Legas ya tabbatar da cewa al’amura sun fara daidaita a jihar bisa yadda ake samun raguwar layuka da karin gidajen mai da suke sayar da man.