Kanin gwamnan Jihar Ebonyi, Mista Austin Umahi, ya yi fatali da mukamin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya masa a matsayin sakataren hukumar tattara kudaden shiga na haraji da rabasu wato ‘Revenue Mobilization Allocation and Fiscal Commission’ (RMAFC).
A sanarwar manema labarai da ya fitar a Abakaliki da ke jihar Ebonyi, Austin Umahi, ya ce nadin ya dace ne a yi ga masu neman aikin yi ko kuma tsoffin ma’aikatan da suka yi ritaya amma ba ga irinsa ba.
Ya bukaci dukkanin wani mutumin da yake da sha’awar samun wannan kujerar da ya tuntubi gwamna Umahi.
“A iya sanina har yanzu babu kowa a kan wannan mukamin.
“Ina mai cike da mika sakon godiya ta ga wadanda suka yi ta turo min sakon taya murna dangane da nadina a matsayin sakataren RMAFC.
“A zahirin gaskiya, kan wannan nuna kauna din, ina bakin cikin sanar da ku cewa na ki amsar nadin da aka min saboda ya dace ne da wadanda suke neman aikin yi ko tsoffin ma’aikatan Gwamnati. Na tabbatar a bisa shekaruna da kwarewata a rayuwa na san abubuwan da suka kamata da rayuwata.
“Don Allah duk wanda yake son kujerar ya nemi gwamna Umahi domin yin abun da ya dace a iya sanina har yanzu mukamin babu kowa a kai.”
Austin Umahi, wadda a baya ya zama dan takarar Sanata a jam’iyyar APC amma daga bisani ya janye wa Gwamna Umahi.
LEADERSHIP ta labarto cewa a ranar Laraba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nada kanin Gwamna Umahi a matsayin sakataren hukumar RMAFC.