Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta rungumar harkokin kimiyya da fahasa, domin kyautata rayuwar dumbin al’ummar da ke fadin jihar ta hanyar bayar da muhimmanci ga harkokin kimiyya da fasaha a jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Kimiyya, fasaha da kere-keren zamani na jihar, Muhammed Tajo Othman, wanda ya jagoranci babban sakatare da daraktocin ma’aikatar zuwa zagayen duba Cibiyar Musulunci ta Kura da Wudil da suke jihar, domin duba injinan wasan kwallon kafa da wasu injinan da aka yi watsi da su.
Tajo Othman ya ce, Gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta sanya hankali sosai wajen ganin ta yi amfani da harkokin kimiyya da fasaha da kere-kere, domin tabbatar da cewa a halin da ake ciki yanzu na kimiyya da fasaha na taimakawa sosai wajen bukatar ci gaba, don haka jihar ba za ta yi wasa da wannan fanni ko kadan ba.
Kwamishinan ya kara dacewa, ziyarar na kunshe ne da manufar duba halin da injinan suke ciki, domin ganin an bi matakan da suka dace wajen gyara su tare da tabbatar da ganin sun dawo sun ci gaba da aiki yadda ya kamata.
“Akwai shirye-shiryen da ake yi na horas da jami’ai ta yadda za su tafi daidai da zamanin, sannan yanzu haka duniya na tafiya ne tare da kwarewar zamani”, in ji shi.
Haka zalika, ya bukaci jami’an da aka horas a cibiyoyin da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen tabbatar da yin amfani da injinan yadda ake bukata. Sannan ya kuma hore su da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen tsayuwa da kafafunsu.
Da suke yin nasu jawabin, mahalarta taron na Kananan Hukumomin da ban da ban sun bayyana cewa, injinan za su iya fitar da balabalan kwallon kafar akalla kimanin guda 100 a kowace rana. Sun kuma kara da cewa, dukkanin Kananan Hukumomin Jihar 44, sun amfani da wadannan cibiyoyi.
Sannan sun kuma roki Gwamnan Jihar, ya samar musu da muhallai na dindindin domin taimaka musu wajen kara jajircewa tare da jan damarar yin aiki yadda ya kamata.
Haka zalika, ababen da kwamishinan ya duba yayin ziyarar tasa sun hada da injin yanka kwallon kafa da jannareto mai girman 15KBA da kuma fatar da ake yin amfani da ita wajen lullebe kwallon da kuma wasu sauran kayayyaki.