ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

by Nuhu Ubale Ibrahim
6 months ago
Sallar

Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah Shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, shugaban na farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka; wannan rubutu ya ƙunshi bayani akan Sallar Idi a bisa fahimtar Mazhabar Malikiyya. Ga bayanin kamar haka.

  • Yadda Sheikh Musa Lukuwa Ya Jagoranci Sallar Idi A Sakkwato
  • Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah

1. Sallar Idi sunna ce mai ƙarfi ta wajibi.

ADVERTISEMENT

2. Liman da mamu za su tafi filin idi bayan rana ta fito, domin suna isa filin idi hantsi ya yi, sai a yi salla.

3. Ana yin Sallar Idi a filin Idi ba a masallaci ba, sai dai idan akwai lalura, to za a iya yi a masallaci, haka nan waɗanda suke a garin Makka za su yi ta ne a Harami.

LABARAI MASU NASABA

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

Menene Hukuncin Yin Aure Da Cikin Shege?

4. Mustahabbi ne mutum ya yi wanka domin sallar Idi.

5. Mustahabbi ne idan an yi wankan a tafi masallaci ba tare da ɓata lokaci ba.

6. Mustahabbi ne a yi ado a sanya turare da sababbin tufafi ga wanda yake da iko.

7. Za a tafi filin Idi ana kabarbari a bayyane har a je filin idi, idan an je ba a yin nafila, za a zauna a ci kaba da kabarbari har liman ya ƙaraso, sai a tsaya da kabarbari. Idan liman yana kabarbari , nan ma mamu za su yi kabarbari idan liman ya yi.

TAMBIHI: Kabarbari aka fi buƙata sama da wa’azi kafin liman ya zo, don Allah a bar al’umma su raya kabarbarbari a Filin Idi.

8. Sallar idi raka’a biyu ce , kuma ana yin karatu a bayya ne, a raka’a ta farko ana yin kabbara bakwai har da kabbarar harama sai liman ya fara karatu, a ta biyu kuma kabbara shida har da ta mikewa. Ana karanta Fatiha da Sabbi a rakar farko a ta biyu kuma Fatiha da Hal’ataka ko kuma makamantansu.

9. Idan mutum bai riski wani abu tare da liman da bai kai raka’a ba, to, zai yi kabbara bakwai a raka’a ta farko kafin ya yi karatu, kuma zai kabbara shida a raka’a ta biyu kafin ya fara karatu kamar yadda liman ya yi.

10. Ba a yin nafila bayan an gama sallar idi.

11. Liman zai yi huɗuba guda biyu, kuma zai zauna a tsakaninsu, haka nan ana so ya yawaita kabarbari a huɗubarsa.

12. Ana so a yi sallar layya da wuri akan ta sallar azubi, domin ana so a ci abinci kafin a tafi karamar salla, ita kuma ta layya sai bayan an dawo.

13. Kabarbari da ake so a yi, laffuzansu suna da yawa kuma za a iya yin kowanne, daga ciki akwai: Allahu Akbar Allahu Akbar La’ilaha illallahu Allahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamdu.

14. Ana so a rinƙa kabarbari a bayan kowacce salla ta farilla sau uku bayan salla da kwana uku, kuma ana so a yawaita zikiri a cikinsu.

15. Mustahabbi ne ga mata da yara idan ba za su je sallar idi ba, to su yi wanka da ado da sanya sababbun kaya idan da hali.

16. Mata su guji caba ado da sanya turare idan za su idi saboda gudun fitina.

17. Makruhi ne mutum ya ƙi yin ado da kwalliyya da gayu a ranar idi wai don gudun duniya, idan kuma ya ƙi yi da sunan addini, to ya zama ɗan bidi’a.

18. Yara da mata za su iya yin wasanni a ranakun idi.

19. Mustahabbi ne mutum ya sabunta hanya wajen dawo gida, watau ya sauya hanya.

Allah ya karɓa mana ibadunmu ya gafarta mana. Amin.

Manazarta:

1~ Muwadda Maliki [shafi 87-90] bugun Mu’assatul Mukhtãr.
2~ Almudauwanatul Kubra [1/223-231] ta Imam Malik Riwayatu Imam Sahnun, bugun Maktabatus Saƙãfati Addiniyyati.
3~ Arrisãlatu [shafi na 71-72] na Abu Zaid Alƙairawãnī,bugun Dãrul Fadīlati.
4~ Attalƙīnu [shafi na 115-116] na Abdulwahab Albagdadi, bugun Dãrul Fadīlati.
5~ Alma’ūnatu [1/233-237] na Abdulwahab Albagdadi, bugun Dãrul Fadīlati.
6~ Alkãfi [shafi na 128-129] na ibnu Abdilbarri, bugun Assahwatu.
7~ Mukhtasul Khalil [shafi na 87] na Shehu Khalil, bugun Dãru Ibnil Jauzī.
8~ Sharhul Iziyyati [shafi na 103-106] na Sharnūbi .
9~ Fathu Rabbil Bariyyati [shafi n 558-566] na Farfesa Masur Sokoto, bugun Maktabatul Imamil Bukhari.
10~ Sirãjus Sãliki [1/135-137] na Al’ujali, bugun Dãrul Fikr
11~ Bulgatus Sãliki [1/175-177] na Ahmad Assãwi, bugun Dãrul Fikr
13. Assharhu Assagir [1/652-660] na Ahmad Addardir, bugun Dãrul Fadīlati.
14~ Takribul Murãdi [shafi na 124-128] na Sulaiman Zamfara, bugun Dãrul Ummati.
15. Jawãhirul Iklil [1/101-104] na Saleh Abdussami’i, bugun Sharikatul Kudsi.

Nuhu Ubale Ibrahim
Abu Razina Paki
Zul-hijja 9,1444H

Sallar
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 21

MASU ALAKA

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa
Fatawa

Menene Hukuncin Yin Aure Da Cikin Shege?

June 21, 2026
Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
Bakon Marubuci

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

May 27, 2026
Next Post
Sallar Bana: Yadda Al’umma Ke Bukukuwa Cikin Firgicin ‘Yan Ta’adda Da Tsadar Rayuwa A Arewa

Sallar Bana: Yadda Al’umma Ke Bukukuwa Cikin Firgicin ‘Yan Ta’adda Da Tsadar Rayuwa A Arewa

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.