Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ya yi murabus daga mukaminsa.
A cewar wani sako da mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa na zamani ga shugaban kasa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce: Timipre Sylva, ya yi murabus daga mukaminsa domin tsayawa takara a zaben gwamnan Bayelsa mai zuwa.”
- Mutum 50 Suka Amfana Da Zakkar Da Wani Bawan Allah Ya Fitar A Kaduna
- Kada Ku Sake Bai Wa Gwamnati Mai Barin Gado Bashi —Abba Ga Bankuna
Sylva zai shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a watan Afrilu.
Timipre Sylva ya kasance tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, inda ya yi wa’adi daya kafin a nada shi minista kuma yana da ‘yancin sake tsayawa takara a wani wa’adin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp