Wasu sassan Nijeriya sun fada cikin duhu sakamakon karancin iskar gas lamarin da ya kara janyo damuwa da tashin hankali hadi da kara lafta matsaloli kan sha’anin wutar lantarki a Nijeriya.
An rawaito cewa a makon jiya ne gwamnatin Nijeriya da kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya suka dauka alhakin karancin samun wutar lantarki a Nijeriya da karancin samun iskar gas a ‘yan makonnin da suka gabata.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mahalarta Ɗaurin Aure 55, Da Kashe Mutane 3 A Katsina
- Tabbas Philippines Ba Za Ta Cimma Yunkurinta Na Kafa “Karamar Da’Ira” A Tekun Kudancin Sin Ba
Bugu da kari a ‘yan watannin baya, gwamnatin ta kuma daura alhakin karancin samun iskar gas kan rage yawan wutar lantarkin da babban kamfanin samar da wutar lantarki ta Niger Delta Power Holding Campani (NDPHC) ta yi ga kamfanonin rarraba wutar lantarki.
Samar da wutar lantarki a Nijeriya ya dogara ne kan manyan tekun ruwa da layukan gas.
Duk da tsawon shekaru da aka shafe a Nijeriya ana fitar da makuden kudade, har yanzu lamarin wutar lantarki na fuskantar matsalolin rashin wadatan ‘yan kasa kuma al’umma sun dogara sosai wajen amfani da wutar lantarki wajen gudanar da harkokin rayuwa da daman gaske.
A karshen shekarar 2023 hukumomin da ke sanya ido kan harkoki wuta da NERC sun cewa karancin gas ne babban matsalar da ke shafan lamarin harkokin lantarki a Nijeriya.
Wannan matsalar na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ta kasance na da arzikin gas tiriliyan 208.83 kwatankwacin kaso 33 na adadin gas da Afrika ke da shi, a cewar babban jami’in gudanarwar NUPRC, Gbenga Komolafe.
Kamar sauran bangarori a Nijeriya, masana’antar samar da wutar lantarki na fuskantar tulin matsalolin da suke kawo tsaiko ga cigabanta.
Da ya ke ganawa da wata kafa a ranar Litinin, Bokaji Tunji, babban mai bada shawara kan harkokin yada labarai wa ministan lantarki, Adebayo Adebalubu, ya ce, gwamnatin tarayya ta hannanta lamarin shawo kan matsalar karancin gas ga GenCos.
A cewarsa, tunin gwamnatin ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalolin ciki har biyan basukan da GenCos ke bi.
“Ministan yana iyaka bakin kokarinsa wajen ganin an shawo kan matsalar, ciki har da biyan basukan da kamfanoni GenCos ke biya da sauran masu ruwa da tsaki.”
“Ina tabbatar muku ministan zai shawo kan matsalar karancin gas zuwa ga kamfanonin da ke rarraba gas din,” ya shaida.
Kazalika, sakataren kamfanonin lantarki, APGC, Joy Ogaji, ta ce, ba ta da masaniyar cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da GenCos domin shawo kan matsalolin gas.
Ogaji, ta ce, da yiyuwar gwamnatin ta tsara matakan da za a bi wajen shawo kan matsalolin da ke addabar kamfanonin samar da wutar lantarki, NESI.
Shi kuma Kunle Olubiyo, shugaban NCPN, ya daura laifin ga gwamnati, ya ce gwamnati ne kawai za ta yi abubuwan da suka dace wajen samun mafita ga matsalolin.